2019: Talakawa ne zasu yanke hukunci kan wanda zai zamo shugaban kasar Najeriya na gaba - Keyamo

2019: Talakawa ne zasu yanke hukunci kan wanda zai zamo shugaban kasar Najeriya na gaba - Keyamo

Festus Keyamo, babban lauya kuma daraktan kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa a titunan kasar za’a yanke hukuncin wanda zai zamo shugaban kasa na gaba.

Ya yi sharhin ne a shafinsa na Twitter, @fkeyamo, a ranar Litinin, 11 ga watan Yuni.

Legit.ng ta bayyana cewa babban lauyan ya ce an fita daga wannan karni da janar din sojoji ke yanke hukuncin wanda zai zamo shugaban kasar Najeriya.

Ga yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter:

KU KARANTA KUMA: 2019: Zuwa yanzu jam’iyyu 13 ke hararar kujeran shugaba Buhari (jerin sunaye)

Idan baza ku manta ba a baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya koka kan cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirya wani makirci na son kama shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel