Wani masoyin kwallon kafa ya ja kafadar Salah yayin daukar hoto a Rasha

Wani masoyin kwallon kafa ya ja kafadar Salah yayin daukar hoto a Rasha

Azaba ya sa dan kwallon kafar Liverpool Mohammed Salah yunkuri cikin gaggawa bayan wani masoyinsa ya kama kafadarsa na hagu dake ciwo yayin da yake kokarin daukar hoto da shi.

Masoyin nasa ya kasace cikin farin ciki yayinda ya hangi Mohammed Salah yana sauka daga motar horo na Masar sannan kuma yayi gaggawan zuwa don suyi hoto inda ya manta cewa har yanzu Salah na jinyar ciwon da ya ji a kafadarsa.

Ba tare da bata lokaci ba Mohammed Salah ya cire hannun masoyin nasa daga kafadarsa sannan masu tsaro suka kare shi cikin dandazon mutanen da suka taru.

Jami’an tsaro sun ture hannun matashin kafi suka yi gaggawan raka Salah domin kada a ji masa ciwo.

Wani masoyin kwallon kafa ya ja kafadar Salah yayin daukar hoto a Rasha

Wani masoyin kwallon kafa ya ja kafadar Salah yayin daukar hoto a Rasha

Wani masoyin kwallon kafa ya ja kafadar Salah yayin daukar hoto a Rasha

Wani masoyin kwallon kafa ya ja kafadar Salah yayin daukar hoto a Rasha

KU KARANTA KUMA: Wasu yan kabilar Igbo 5 sun musulunta (hotuna)

Idan dai baza ku manta ba Mohammed Salah ya ji rauni a kafadarsa a gasar cin kofi na karshe bayan wani kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos ya far masa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel