Harin kunar bakin wake cikin dare ya hallaka mutane 3 a Maiduguri

Harin kunar bakin wake cikin dare ya hallaka mutane 3 a Maiduguri

Akalla mutane 3 sun rasa rayukansu kuma 4 sun jikkata a wani harin kunar bakin wake da yan Boko Haram suka kai cikin dare a garin Maiduguri, jihar Borno, jami’un tsaro sun tabbatar da haka.

Wani mumunan hari ya auku ne a shahrarriyar hanyar Baga, musamman a garejin Barka da zuwa na Maiduguri misalin karfe 1:30 na dare inda wani dan kunar bakin wake ya tayar da Bam da ya hallakashi da wasu mutane 3.

A wani wasika da idon shaida ya tabbatarwa manema labarai, yace: “Wani harin kunar bakin wake ya sake faruwa a yau (Lahadi) misalin karfe 1:35 na dare a Baga,”

"Mutane 3 sun hallaka da dan kunar bakin waken, yayinda wasu 4 suka jikkata.”

Hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa an kai hari Bam a Baga amma basu bayyana adadin mutanen da suka mutu ba. It would be recalled that two days ago, a lone bomber killed self at the crowded post office area in heart of Maiduguri city.

Zaku tuna cewa kwanaki biyu da suka wuce, wani dan kunar bakin wake ya hallaka kansa a garin Maduguri.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel