Sabuwar PDP ba za ta balle daga APC ba - Apugo

Sabuwar PDP ba za ta balle daga APC ba - Apugo

- Mamba na kungiyar sabuwar PDP yayi Karin haske akan zargi da ake yin a ficewarsu daga APC

- Apugo ya jadadda cewa suna nan daram dakam babu inda za su

- Ya bukaci mambobin sabuwar PDP das u hada kansu su gana da shugaba Buhari

Wani mamba na kungiyar sabuwar PDP wanda ya zama mamba a kungiyar amintattu na APC, Prince Benjamin Apugo, ya ba da tabbacin cewa hukuncin su na dakatar da cigaba da tattaunawa da fadar shugaban kasa ba zai kai su ga ballewa daga jam’iyya mai mulki ba.

Apugo wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Umuahia, a jiya ya bayyana cewa babu wata Baraka a APC, yace akwai bukatar mambobin sabuwar PDP su hada kansu sannan su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan zargin wariya da ake nunawa mambobinta.

Sabuwar PDP ba za ta balle daga APC ba - Apugo

Sabuwar PDP ba za ta balle daga APC ba - Apugo

Ya kuma yi roko ga shugaban kasa da ya samar da ofishin shugaban kasa a jihohin da ba APC ke mulki ba; kamar irin wanda Shehu Shagari yayi a lokacin jumhutiya na biyu.

Mambobin kungiyar sabuwar PDP din sun hada da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da sauransu.

KU KARANTA KUMA: 2019: Zuwa yanzu jam’iyyu 13 ke hararar kujeran shugaba Buhari (jerin sunaye)

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sabuwar PDP kungiyar adawar APC ta bayyana cewa tana jiran jam’iyya mai mulki da shugaban kasa Muhammadu Buhari suyi kira gare su, sannan kuma ta tunasar da jam’iyyar cewa lokaci na shirin kure masu.

Da yake magana a madadin gamayyar kungiyar a wani hira da Channels TV, Alhaji Kawu Baraje shugaban kunciyar ya bayyana cewa kungiyar sabuwar PDP a shirye take ta saura a jam’iyyar APC idan har aka cika sharudan ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel