Muna jiran APC da Buhari kafin mu yanke hukunci – Sabuwar PDP

Muna jiran APC da Buhari kafin mu yanke hukunci – Sabuwar PDP

Sabuwar PDP kungiyar adawar APC ta bayyana cewa tana jiran jam’iyya mai mulki da shugaban kasa Muhammadu Buhari suyi kira gare su, sannan kuma ta tunasar da jam’iyyar cewa lokaci na shirin kure masu.

Da yake magana a madadin gamayyar kungiyar a wani hira da Channels TV, Alhaji Kawu Baraje shugaban kunciyar ya bayyana cewa kungiyar sabuwar PDP a shirye take ta saura a jam’iyyar APC idan har aka cika sharudan ta.

Legit.ng ta lura cewa bayan gayyatar da hukumar yan sanda ta aikewa Sanata Bukola Saraki, kungiyar wacce ke dauke da shugaban majalisar dattawa, kakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da akalla gwamnoni biyu da sanatoci sama da 20 ta janye tattaunawa da jam’iyyar.

Suna ganin gayyatar da yan sanda suka yi masa a matsayin makoma mara kyau a jam’iyyar APC.

Muna jiran APC da Buhari kafin mu yanke hukunci – Sabuwar PDP

Muna jiran APC da Buhari kafin mu yanke hukunci – Sabuwar PDP

Sabuwar PDP ta bayar da wa’adi ga APC da shugaba Buhari kan su magance lamuran bincike da bangaranci ga mambobin ta wanda suka bayar da gagarumin gudunmawa wajen nasarar jam’iyyar a 2015.

KU KARANTA KUMA: 2019: Zuwa yanzu jam’iyyu 13 ke hararar kujeran shugaba Buhari (jerin sunaye)

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wasu majiyoyi sunyi has ashen cewa mabiya sabuwar jam’iyyar PDP za su bar APC a ranar 23 ga watan Yuni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel