Idan ajali yayi kira: Mutane 7 yan gida daya sun rasa rayukansu a wani matsarin mota

Idan ajali yayi kira: Mutane 7 yan gida daya sun rasa rayukansu a wani matsarin mota

Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a jihar Enugu, ya rutsa da wasu mutane su bakwai yan gida daya, inda dukkaninsu suka rigamu gidan gaskiya take yanke, inji rahoton jaridar Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Ebere Amaraizu ne ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda yace ya faru ne a ranar Lahadi da sanyin safiya, misalin karfe 8.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sauka kasar Moroko, an masa tarbar girma

Kaakakin yace wata mota kirar Toyota camry ce ta yi taho mu gama da wata motar sufuri Toyota Hiace, a yayin da dukkaninsu ke cikin tsananin gudu, nan take mutanen cikin Camry su bakwai yan gida daya suka mutu, yayin da mutum guda daga dayar motar ya rasu shima.

Zuwa yanzu an mika gawar mamatan zuwa dakin ajiyan gawarwaki, haka nan sauran wadanda suka jikkata daga cikin motar sufurin na samun kulawa a babbar asibitin koyarwa na jami’ar jihar Enugu.

Daga karshe Kaakaki Ebere ya bada tabbacin zasu soma bincike kan lamarin ba tare da bata lokaci ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel