Yadda Buhari, Osinbajo, Tinubu da sauran su suka yi fatali da jam'iyyar APC bayan sun ci zabe

Yadda Buhari, Osinbajo, Tinubu da sauran su suka yi fatali da jam'iyyar APC bayan sun ci zabe

Wani bincike da gidan jaridar Premium Times yayi da kuma muka samu ya bayyana cewa jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya da suka hada da Buhari Osinbajo, Tinubu da ma sauran su dukkan su sun yi fatali da biyan kudin jam'iyya tun da suka yi nasarar lashe zaben su a 2015.

Majiyar ta mu dai ta bayyana cewa ta samu wannan bayanin ne a cikin rahoton yadda ta kashe kudaden ta da ta kaiwa hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Yadda Buhari, Osinbajo, Tinubu da sauran su suka yi fatali da jam'iyyar APC bayan sun ci zabe

Yadda Buhari, Osinbajo, Tinubu da sauran su suka yi fatali da jam'iyyar APC bayan sun ci zabe

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ba ta lafiya - Sanata Dino

Legit.ng ta samu cewa sai dai masana da suka tofa albarkacin bakin su game da hakan sun bayyana shakkun su a kan gaskiyar rahoton.

A wani labarin kuma, Sanannen Sanatan nan dake wakiltar al'ummar mazabar jihar Kogi ta yamma a majalisar dattijai Sanata Dino Melaye ya kwatanta jam'iyyar su ta APC mai mulki da mutumin da bai lafiya, magashiyyan.

Sanata Dino ya bayyana hakan ne a lokacin da ake fira da shi a gidan Talabijin din nan mai zaman kan sa na Channels a cikin shirin 'Siyasar mu a Yau'.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel