Gwamnatin tarayya zata tantance malaman makaranta a watan Disamba

Gwamnatin tarayya zata tantance malaman makaranta a watan Disamba

- Gwamnatin tarayya na shirye-shiryen gudanar da tankade da rairaya a harkar ilimi

- Wannan dai na zuwa domin yi garanbawul a fannin koyo da koyarwa musamman a makarantun Firamare da na Sakandire

A jiya ne gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata sallami duk malamin makaranta daga aiki mutukar ya gaza cinye jarrabawar da hukumar shirya jarrabawa ta malamai zata shirya a watan Disambar shekara ta 2019.

Za'a kuma: Gwamnatin Tarayya zata kori Malaman Makaranta daga aiki a watan Disamba

Za'a kuma: Gwamnatin Tarayya zata kori Malaman Makaranta daga aiki a watan Disamba

Sakataren hukumar ilimi na kasa baki daya ne ya bayyana sanarwar a Abuja, a yayin wata horaswa da ake wa malamai a birnin tarayya, inda yace tabbas dole ne a kara bunkasa harkar ilimi a kasar nan musamman bangaren abinda ya shafi koyo da koyarwa.

Sannan ya kara da cewa a halin yanzu akwai mutane da dama wadanda suke da nagarta kuma suna jiran gwamnati a matakin jiha da tarayya da ta basu aiki.

Don haka ya ce gwamnati zata kawo dukkan abubuwan da malaman zasu na amfani da shi wajen koyarwa a makarantun gwamnati.

KU KARANTA: Kurunkus: Ba sauran SAK a zabuka masu zuwa inji Shugaba Buhari

Farfesa Josiah Olusegun Ajiboye wanda shi ne mai kula da duk wani sha'ani da ya shafi rijistar malamai akan jarrabawar yace malamai gudu dubu 22,000 ne zasu zana jarrabwar a wannan wata, kuma malamai dari 900 sune zasu zana jarrabawa a birnin tarayya. Sannan ya kara da cewa za a sake zana wata jarrabawar a watan Satumba.

haka nan kuma hukumar tana nan ta shirye-shiryen yadda zata tsaro tambayoyi musamman ga malaman da suke koyarwa a makarantun Labaraci.

Za'a kuma: Gwamnatin Tarayya zata kori Malaman Makaranta daga aiki a watan Disamba

Za'a kuma: Gwamnatin Tarayya zata kori Malaman Makaranta daga aiki a watan Disamba

A watannin baya ne dai gwamnatin jihar Kaduna ta shirya wata jarrabawa makamaciyar wannan wanda hakan yayi sandiyyar korar malamai da yawan gaske daga bakin aiki sakamakon rashin nasara da su kayi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel