Ba zamu koma teburin sulhu da APC ba har sai suka wadannan sharuda – ‘Yan nPDP

Ba zamu koma teburin sulhu da APC ba har sai suka wadannan sharuda – ‘Yan nPDP

‘Yan nPDP karkashin jagorancin Kawu Baraje sun nuna sha’awar su na komawa teburin sulhu da shugabancin jam’iyyar APC matukar an cika wasu sharuda da suka zayyana.

Baraje, tsohon shugaban jam’iyyar PDP, ne ya bayyana hakan a jiya, Asabar, yayin da ya bayyana a wani shirin gidan Talabijin a Abuja .

Ya bayyana cewar mambobin su har yanzu na son a koma teburin sulhu domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin jam’iyyar APC mai mulki tare da bayyana cewar tun farko sun aike da takardar korafi ga jam’iyyar ne saboda kishin da suke mata.

Ba zamu koma teburin sulhu da APC ba har sai suka wadannan sharuda – ‘Yan nPDP

Yayin wani zaman sulhu tsakanin ‘yan nPDP da Osinbajo

Saidai Baraje ya bayyana cewar, komawar su teburin sulhu ya dogara da samun tabbacin cewar ba za a cigaba da muzgunawa ‘ya’yan ta ko cigaba da yi masu barazana ba.

A shirye mu ke mu koma teburin sulhu, saboda muna son sulhu ne tun farko mu ka rubuta takardare koke zuwa ga uwar jam’iyya. Saidai ba zamu koma tattaunawa ba har sai an samu canji ta fuskar yadda gwamnati ke mu’amalantar mambobin mu,” a cewar Baraje.

DUBA WANNAN: Ka miika kan ka a bincike ka idan kana da gaskiya - Wani gwamna ya shawarci Obasanjo

Sannan ya cigaba da cewa, “ni jagora ne kawai, kuma zan koma wurin mutanen da nake wakilta duk lokacin da muke bukatar daukan wani mataki dangane da makomar mu a siyasar Najeria.

A satin da ya gabata ne ‘yan nPDP suka bayyana cewar sun fita daga sulhun da suke yi da jam’iyyar APC sun a masu zargin cewar APC na da wani mugun nufi a kan ‘ya’yan ta duk da irin gudunmawar da suka bawa jam’iyyar hart a kai ga nasara a zaben 2015.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel