Hakar wani ɗan ƙunar bakin wake ya gaza cimma ruwa a Maiduguri, ya kashe kansa shi kadai

Hakar wani ɗan ƙunar bakin wake ya gaza cimma ruwa a Maiduguri, ya kashe kansa shi kadai

- Jami'an tsaro san samu galaba a cigaba da yaki da 'yan ta'addan Boko Haram

- Wannan nasara tazo bayan tsorata da ganinisu da wani dake dauke da bam yayi, kawai sai ya tashi bam din ya kashe kansa da kansa

Tsoro da razana ya sanya wani dan ƙunar baƙin wake sakin kunamar dake ɗane da Bam ɗin jikinsa a kusa babbar kasuwar Monday Market dake Maiduguri babban birnin jihar Borno a jiya da daddare.

Hakar wani ɗan ƙunar bakin wake ya gaza cimma ruwa a Maiduguri, ya kashe kansa shi kadai

Hakar wani ɗan ƙunar bakin wake ya gaza cimma ruwa a Maiduguri, ya kashe kansa shi kadai

Lamarin dai ya faru ne a jiya Asabar da misalin karfe 7:15pm na dare a cewar wani mataimakin Sufritandan ƴan sanda mai suna Edet Okon.

KU KARANTA: Mutum 1 ya rasa ransa, an cafke 2 a wani rikici da ya barke a kaduna

"Bayan ganin tulin jami'an tsaro da aka jibge a kusa da Ofishin aikewa da saƙonni na Post Office daura da gidan Man Oando, ɗan ƙunar bakin sai ya firgita yayin da ya nufi kasuwar Monday Market domin tayarwa, kawai sai ya saki kunamar bam ɗin dake jikinsa wanda hakan yayi sandiyyar mutuwarsa shi kaɗai." A jawabin Edet.

Tuni dai "Kwamishinan ƴan sanda na jihar Damian Chukwu ya aike da jami'an EOD domin tabbatar da lafiyar wurin don kowa ya koma tafiyar da harkokinsa kamar yadda ya saba. Sannan ya tabbatar da aniyar rundunar ƴan sanda na kasancewa cikin shirin ko ta kwana a yayin da gudanar da Azumin Ramadan".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel