Sojoji da ƴan sanda sunyi haɗin gwuiwa wajen wani muhimmin aikin bajinta

Sojoji da ƴan sanda sunyi haɗin gwuiwa wajen wani muhimmin aikin bajinta

- Hadin gwuiwar jami'an tsaro yayi sanadiyyar samun nasara gagaruma

- Bayan artabu da 'yan bindiga akarshe sunyi galaba a kan gugun masu garkuwa da Mutane

- Yanzu haka dai an mika wadanda aka ceto bayan garkuwa da su zuwa hannun jami'an 'yan sanda.

wani sumamane hadin guiwa da aka gunadar tsakanin sojoji da yan sanda, an samu nasarar ceto wani dan kasuwar man fetur da matarsa da kuma wasu mutane guda shida daga hannun masu garkuwa da mutane a ranar Juma'ar da ta gabata.

Sojoji da ƴan sanda sunyi haɗin gwuiwa wajen wani muhimmin aikin bajinta

Sojoji da ƴan sanda sunyi haɗin gwuiwa wajen wani muhimmin aikin bajinta

Jami'an tsaron bisa jagorancin umarnin hukumar tsaro ta jihar Ekiti sun gunadar da sumamen ne a dajin da ake rike da mutanen da aka yi garkuwar da su.

Wata majiya ta bayyana cewa an jiyo karar harbe-harben bindiga a tsakanin masu garkuwa da mutane da kuma jami'an tsaron, wanda ya dauki tsawon wani lokaci ana bata-takashi.

Majiyar ta ce masu garkuwar sun bukaci da iyalan wanda aka kama da su biya kudi har naira miliyan 20, wanda daga bisani suka rage zuwa miliyam 15.

Dan kasuwar mai suna Mr. D.Alalade an yi garkuwa da shi da mai dakinsa ne da misalin karfe 4:00 na yamma a daidai wurin Erik da Economic, wanda masu garkuwar suka yi shiga cikin kayan sojoji.

Mr. Alalade ya kasance shi ne shugaban kamfanin man fetur da iskar gas na BOVAS dake jihar ta Ekiti.

KU KARANTA: Ka mika kan ka kawai a bincike ka, ka daina raki – Wani gwamna ya shawarci Obasanjo

A cikin wani jawabi da kakakin hadin guiwar Manjo Ojo Adenegan ya fitar a jiya ya bayyana cewa, an yi nasarar ceto mutanen da aka yi garkuwar dasu bayan an shafe wasu lokuta an bata-takashi da masu garkuwar.

Dama dai tuni garkuwa da mutane da kuma fashi-da-makami ya zamo ruwan dare a kan hanyar Efon da Erinmo dake da makwabtaka da jihar Osun.

An bada rahoton cewa mutane masu garkuwar sun kashe mutane uku tare da yin awon da wasu a satin da ya gabata.

Wannan daji da yake da iyaka da jihar Osun ya kasance wata matattara ta masu aikata laifi musamman fashi-da-makami da kuma yin garkuwa da mutane daban-daban wanda daga ciki har da manyan mutane.

A kwanakin baya ma anyi garkuwa da sakataren jam'iyyar PDP na jihar wanda shi ma ya dauki lokaci kafin a sako shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel