NAFDAC tayi babbar nasarar kama muggan kwayoyin da aka hana shigowa masu yawan gaske

NAFDAC tayi babbar nasarar kama muggan kwayoyin da aka hana shigowa masu yawan gaske

- A yunkurin mahukunta na hana shigowa da muggan kwayoyin da aka hana amfani da su, hukumar kula da kuma tabbatar da lafiyar abinci da magunguna ta kasa ta damke kwantenoni 35 da miyagu su kayi yunkurin shigowa da su ta iyakokin kasar

- A watan da ya gabata ne Gwamnatin Najeriya ta haramta sarrafawa da shigo da duk wani magani mai dauke da sinadarin codeine a cikinsa

Shugabar hukumar lura da harhada abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) Farfesa Moji Adeyeye ta ce hukumar tayi nasarar kama kwantenoni har 35 cike da kwayoyin Tramadol a mashigar shigo da kaya kasar nan daban-daban.

NAFDAC tayi babbar Nasarar kama kwayoyin da aka hana shigowa da su har kwantena 35

Farfesa Moji Adeyeye

Farfesa Adeyeye ta bayyana hakan ne ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) yau Lahadi a Abuja.

Sai dai ta ce daga cikin 35 din da suka kama har yanzu 9 ne kacal suka kai ga shiga hannunsu kuma tuni sun lalata su gaba daya.

KU KARANTA: Da sauran tsalle: ‘Yan sanda sun kara gano wata alaka mai karfi tsakanin ‘yan fashin Offa da Saraki

"Muna aiki sosai tare da hukumar hana fasa kwauri ta kasa (NCS) suna gayyatar mu a duk lokacin da suka kama kwantenar dake dauke da kwayoyin Tramadol. Ya zuwa yanzu mun kama kwantenoni 35, kuma har mun lalata 9 daga cikinsu".

A saboda haka ne Farfesar ta yi kira ga hukumar hana fasa kwaurin ta kasa da ta rage jan kafa wajen mikowa hukumar ragowar da suka rage a wurinta.

Shugabar NAFDAC din ta ce kwayar Tramadol magani ne mai amfani amma matasan Najeriya sun mayar da shi abin sha ba tare da umarnin likita ba.

NAFDAC tayi babbar Nasarar kama kwayoyin da aka hana shigowa da su har kwantena 35

NAFDAC tayi babbar Nasarar kama kwayoyin da aka hana shigowa da su har kwantena 35

Daga nan ne Adeyeye da yabawa yunkurin Gwamnati na hana sarrafawa da kuma shigo da maganin Codein wanda shi ma bai kamata a sha shi ba tare da izinin likita ba.

Sannan ta kuma tabbatar da cewa hukumar ta shirya tsaf yanzu fiye da lokutan baya don magancce jabun magunguna a kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel