Idon wasu ƴan sanda ya raina fata bayan an kama su suna aikata wani abu, karanta kaji

Idon wasu ƴan sanda ya raina fata bayan an kama su suna aikata wani abu, karanta kaji

- Wasu 'yan sanda sun yi wiki-wiki bayan fara tuhumarsu da yiwa wani Mutuma barbaden barkonon tsuhuwa

- Kuma zasu iya fuskantar hukuncin ragin mukami ko na kora daga aiki baki daya

- Asirin 'yan sandan dai ya tonu ne bayan sakin wani bidiyo a kafar sadarwa ta zamani

Wasu ƴan sanda biyu sun shiga tasku bayan da aka kama su suna barbaɗawa Mutane burbushin barkonan tsohuwa a yankin Ojota na jihar Legas.

Idon wasu ƴan sanda ya raina fata bayan an kama su suna aikata wani abu, karanta kaji

kwamishinan ƴan sanda na jihar ta Legas Edgal Imohimi

An kama ƴan sandan ne masu suna Momoh Sulaiman mai muƙamim Sufeto da kuma Sajan Monday Emmanuel bayan da wani bidiyo da aka ɗauke su ya shahara a kafar sadarwar zamani.

A saboda haka na kwamishinan ƴan sanda na jihar ta Legas Edgal Imohimi ya bada umarnin a tabbatar an zakulo su. Kakakin rundunar Chike Oti ya shaida a cikin wani jawabi ga manema labarai.

Tun farko dai kafar sadarwar OAKTV ce ta wallafa shi, sannan an rubuta a cikin bidiyon cewa, ƴan sandan da suka gagara kamuwa bayan kuma jami'an ƴandan SARS sun harbe shi a garin ƴan China dake Ojoto na jihar Legas.

KU KARANTA: Hakar wani ɗan ƙunar bakin wake ya gaza cimma ruwa a Maiduguri, ya kashe kansa shi kadai

A bisa haka ne kwamishinan ya kafa wata rundunar bincike ta Command X Squad wanda su kayi haɗin gwuiwa da Ofishin shiyyar Ogudu karkashin CSP Gbenga Olurunfemi domin binciko su.

"Bayan zurfafa bincike ne muka gano sunan wanda suka barbaɗawan sunan shi Ademuwagun Tamitope Solomon, sannan kuma ba harbinsa aka yi ba kamar yadda bidiyon ya nuna, illa dai kawai barbaɗen barkonon tsohuwa da ayarin ƴn sintirin da Sufeto Momoh Sulaiman da kuma mataimakinsa Sajan Monday Emmanuel suke jagoranta. Amma ya zuwa yanzu wanda akaiwa barbaɗen lafiyarsa kalau".

Waɗanda ake zargin dai tuni suna hannu tun bayan da aka bayar da umarnin bincike don a gano sj har ma an fara tuhumarsu a jiya. "Kuma mutuƙar aka same su da laifin saɓawa dokar aiki da cin zalin Mutum ba gaira ba saba, zasu fuskanci hukunci mai tsanani wanda ka iya kaiwa ga kora daga aiki". Kakakin rundunar Chike ya tabbatar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel