Da sauran tsalle: ‘Yan sanda sun kara gano wata alaka mai karfi tsakanin ‘yan fashin Offa da Saraki

Da sauran tsalle: ‘Yan sanda sun kara gano wata alaka mai karfi tsakanin ‘yan fashin Offa da Saraki

A cigaba da binciken da take gudanarwa a kan ‘yan fashin da suka tafka barnar rayuka da dukiyoyin al’umma a garin Offa, jihar Kwara, hukumar ‘yan sanda ta kara gano cewar, 5 daga cikin shugabannin ‘yan fashin sun halarci bikin diyar Bukola Saraki, shugaban majalisar dattijai.

'Yan fashin sun amsa cewar tabbas sun halarci bikin diyar Bukola da aka yi wasu watanni kafin fashin garin Offa.

A wani jawabi da hukumar ‘yan sanda ta fitar, ta bayyana cewar 3 daga cikin ‘yan fashin na daga cikin mutanen da suka raka Saraki ziyarar jaje da ta’aziyya ga mutanen garin Offa bayan fashin na ranar 5 ga watan Afrilu.

Da sauran tsalle: ‘Yan sanda sun kara gano wata alaka mai karfi tsakanin ‘yan fashin Offa da Saraki

Da sauran tsalle: ‘Yan sanda sun kara gano wata alaka mai karfi tsakanin ‘yan fashin Offa da Saraki

Tuni hukumar ‘yan sanda ta bukaci ya bayyana a gaban ta domin wanke kan sa daga zargin hannun sa cikin fashin garin Offa kafin daga bisani ta janye gayyatar tare da bukatar shi ya rubuto hujjojin kare kan sa zuwa ga hukumar cikin sa’o’i 48.

Bukola Saraki ya musanta cewar yana da hannu a cikin fashin duk da har yanzu bai musanta batun cewar ‘yan fashin na yi masa aiki ba.

DUBA WANNAN: Wata kalma cikin wasikar Buhari ta saka Sanatoci kyalkyala dariya

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar, a ranar Alhamis ne, Alhamis, 7 ga watan Yuni, Idris ya sami sahalewar babbar kotun Najeriya karkashin mai shari’a, John Tsoho, domin shigar da karar majalisar da kuma Bukola Saraki domin fara sauraro a gaban ta.

Ibrahim Idris, babban sifeton rundunar ‘yan sanda na kasa yam aka majalisar dattijai da shugaban ta, Bukola Saraki, gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja bisa bayyana shi a matsayin makiyin dimokradiyya da bai dace da rike wani ofishi na shugabancin jama’a ba da majalisar ta yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel