Kurunkus: Ba sauran SAK a zabuka masu zuwa inji Shugaba Buhari

Kurunkus: Ba sauran SAK a zabuka masu zuwa inji Shugaba Buhari

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya umurci yan Najeriya musamman ma matasa da su yi fatali da umurnin da ya bayar a lokutan zabukan da suka gabata na yin Sak yanzu su zabi duk wanda suka ga ya cancanta a zaben 2019 mai zuwa.

Shugaban kasar dai ya bayyana hakan ne a shafin sa na dandalin sadarwar zamani ta Tuwita a ranar Juma'ar da ta gabata jim kadan bayan kammala tattaunawar sa da wasu zababbun zakakuran matasa musulmai a fadar sa.

Kurunkus: Ba sauran SAK a zabuka masu zuwa inji Shugaga Buhari

Kurunkus: Ba sauran SAK a zabuka masu zuwa inji Shugaga Buhari

KU KARANTA: An kara samun wanda zai kara da Buhari a 2019

Legit.ng ta samu cewa shugaban kasar ya bayyana cewa: "A jiya ne dai na sha ruwa tare da wasu zakakuran matasa daga sassa daban-daban na Najeriya a fannonin rayuwa da dama wadanda kuma na ba shawarar su fito su zabi dukkan wadanda suka ga ya dace ya jagorance su a zaben 2019.

Daman dai tuni mutane sun zura ido sun kuma bude kunnuwan su su ga cewar ko shugaban kasar zai sake umuratar jama'a da su zabi dukkan 'yan jam'iyyar sa a zben 2019 kamar yadda yayi a 2015 ko kuwa a'a.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel