Sai mun Dakatar da duk wata Gudanarwa ta Fadar Shugaban Kasa muddin aka taba Obasanjo - ADC

Sai mun Dakatar da duk wata Gudanarwa ta Fadar Shugaban Kasa muddin aka taba Obasanjo - ADC

Jam'iyyar ADC (Africaan Democratic Congress) ta yi gargardi ga gwamnatin tarayya da cewa za ta dakatar da duk wata gudanarwa da fadar shugaban kasa dake garin Abuja muddin aka taba tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo.

Shugaban jam'iyyar na kasa, Cif Okey Nwosu, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai na jaridar The Punch ta hanyar wayar tarho a ranar Juma'ar da ta gabata.

Nwosu yake cewa, baya ga gazawar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na rashin cika alkawurranta na yakin neman zabe, a yanzu kuma ta dauki wani sabon salo na tozarta mambobin jam'iyyun adawa wajen tursasa su akan mara ma ta baya.

Sai mun Dakatar da duk wata Gudanarwa ta Fadar Shugaban Kasa muddin aka taba Obasanjo - ADC

Sai mun Dakatar da duk wata Gudanarwa ta Fadar Shugaban Kasa muddin aka taba Obasanjo - ADC

Ya ci gaba da cewa, a yayin da Obasanjo ya goyi bayan shugaba Buhari a zaben 2015, an mutunta ta shi da karamci na cewar yana goyan canji daga mulkin kama karya na jam'iyyar PDP, sai gashi yanzu ana tozarta shi tamkar wani dan ta'adda sakamakon rashin goyon bayan kudirin shugaba Buhari na sake tsayawa takara a zaben 2019.

A sanadiyar haka ne jam'iyyar ta yi furucin gargadi da cewar ba za ta lamunci duk wani lahani da zai samu tsohon shugaban kasar ba sakamakon tozarcin da gwamnatin shugaba Buhari ke yi a gare sa.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin shugaba Buhari na zargin tsohon shugaban kasar da handame Dalar Amurka Biliyan 16 na kudaden gyaran wutar lantarki a lokacin gwamnatin sa wanda wannan haka ta cimma ruwa ba a kasar nan kamar yadda shugaba Buhari ya bayyana.

KARANTA KUMA: Obasanjo: Mai Laifi ne kadai zai sanya Damuwa a ransa - Gwamnatin Tarayya

Sai dai wasu kungiyoyi biyu masu kare hakkin dan Adam sun bayyana cewa, Obasanjo ya kasance cikin shirin fuskatar shari'a yayin da binciken hukumar EFCC ya bankado sheda ta rashin gaskiya dangane da yadda aka tafiyar da wannan makudan kudade.

Jagoran kungiyar SERAP mai kare hakkin dan Adam, Adetokunbo Mumini ya bayyana cewa, babatun tsohon shugaba Obasanjo da cewa shugaba Buhari na neman tozarta shi baya da wani tushe ballantana madogara, inda ya ce dole hukumomin hana yiwa tattalin arziki zagon kasa su sauke nauyin da ya rataya a wuyan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel