Rikita-Rikita: 2 daga cikin gaggan barayin da suka fasa bankuna a garin Offa sun yi layar zana

Rikita-Rikita: 2 daga cikin gaggan barayin da suka fasa bankuna a garin Offa sun yi layar zana

Kawo yanzu dai ana cikin zaman dar-dar ne biyo bayan labari mai daga hankalin da muke samu na cewa biyu daga cikin gaggan barayin bankunan nan na garin Offa watau Michael Adikwu da Kayode Opadokun sun yi batan dabo a hannun 'yan sanda.

Mun samu da cewa da jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Jimoh Moshood yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata, ya zayyana barayin biyu tare da wasu sauran akalla ashirin da yace rundunar ta 'yan sanda na zargin su da fasa bankuna.

Rikita-Rikita: 2 daga cikin gaggan barayin da suka fasa bankuna a garin Offa sun yi layar zana

Rikita-Rikita: 2 daga cikin gaggan barayin da suka fasa bankuna a garin Offa sun yi layar zana

KU KARANTA: Mashahurin mai kudi a Najeriya ba ba Buhari kyautar motoci 2

Legit.ng ta samu cewa sai dai tun daga ranar, har yanzu ba'a kara ganin barayin biyu ba duk kuwa da sake haskawa manema labarai sauran da akayi wanda hakan yayi matukar tayar da hankalin jama'a.

A wani labarin kuma, Sanannen Sanatan nan dake wakiltar al'ummar mazabar jihar Kogi ta yamma a majalisar dattijai Sanata Dino Melaye ya kwatanta jam'iyyar su ta APC mai mulki da mutumin da bai lafiya, magashiyyan.

Sanata Dino ya bayyana hakan ne a lokacin da ake fira da shi a gidan Talabijin din nan mai zaman kan sa na Channels a cikin shirin 'Siyasar mu a Yau'.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel