Jam'iyyar mu ta APC ba ta lafiya, tana gargarar mutuwa - Dino Melaye

Jam'iyyar mu ta APC ba ta lafiya, tana gargarar mutuwa - Dino Melaye

Sanannen Sanatan nan dake wakiltar al'ummar mazabar jihar Kogi ta yamma a majalisar dattijai Sanata Dino Melaye ya kwatanta jam'iyyar su ta APC mai mulki da mutumin da bai lafiya, magashiyyan.

Sanata Dino ya bayyana hakan ne a lokacin da ake fira da shi a gidan Talabijin din nan mai zaman kan sa na Channels a cikin shirin 'Siyasar mu a Yau'.

Legit.ng ta samu cewa Sanatan ya kuma kara da cewa shi babban abunda ke damun sa ma shine yadda jam'iyyar ke ta kara yin nisa da zukatan talakawan kasar a kullum.

A wani labarin kuma, Kawo yanzu dai ana cikin zaman dar-dar ne biyo bayan labari mai daga hankalin da muke samu na cewa biyu daga cikin gaggan barayin bankunan nan na garin Offa watau Michael Adikwu da Kayode Opadokun sun yi batan dabo a hannun 'yan sanda.

Mun samu da cewa da jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Jimoh Moshood yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata, ya zayyana barayin biyu tare da wasu sauran akalla ashirin da yace rundunar ta 'yan sanda na zargin su da fasa bankuna.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel