An kara samun dan takarar kujerar shugabancin kasar Najeriya a zaben 2019

An kara samun dan takarar kujerar shugabancin kasar Najeriya a zaben 2019

Labarin da muke samu da dumin sa na tabbatar mana da cewa kawo yanzu dai an kara samun wani dan Najeriya da ya fito ya bayyana ra'ayin sa na neman takarar kujerrar shugaban kasa a zaben 2019 mai zuwa.

Wanda ya bayyana ra'ayin nasa game da takarar kamar yadda muka samu shine tsohon gwamnan jihar Kuros Ribas watau Mista Donald Duke.

An kara samun dan takarar kujerar shugabancin kasar Najeriya a zaben 2019

An kara samun dan takarar kujerar shugabancin kasar Najeriya a zaben 2019

KU KARANTA: Jami'an kwastam sun kafa tarihi a Najeriya

Legit.ng ta samu cewa Mista Donald Duke din dai ya bayyana ra'ayin nasa ne a yayin da yake gabatar da jawabin sa a wajen bikin yaye daliban jami'ar Najeriya dake garin Nsukka na jihar Enugu.

A wani labarin kuma, Sanannen Sanatan nan dake wakiltar al'ummar mazabar jihar Kogi ta yamma a majalisar dattijai Sanata Dino Melaye ya kwatanta jam'iyyar su ta APC mai mulki da mutumin da bai lafiya, magashiyyan.

Sanata Dino ya bayyana hakan ne a lokacin da ake fira da shi a gidan Talabijin din nan mai zaman kan sa na Channels a cikin shirin 'Siyasar mu a Yau'.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel