Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tafi kasar Maroko gobe Lahadi

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tafi kasar Maroko gobe Lahadi

Shugaba Muhammadu Buhari zai yi bulaguron kwana 2 masarautar Maroko a gobe Lahadi, 10 ga watan Yuni, 2018.

Game da cewar mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, shugaba Buhari zai tafi Maroko ne bisa ga gayyatan mai martaba sarkin Maroko, King Mohammed VI, domin tattaunawa kan tattalin arzikin kasashen biyu da suka fara yayinda sarkin ya kawo ziyara Najeriya a Disamban 2016.

Jawabin yace: “Shugaba Muhammadu Buhari zai yi tafiyan kwana 2 masarautar Maroko ranan Lahadi. Zai tafi tare da gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, da gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru da wasu manyan jami’an gwamnati.”

“Zaku tuna cewa an yi yarjejeniya tsakanin Najeriya da Maroko a watan Disamban 2016 domin farfado da masana’antun takin zamani. Zuwa yanzu an farfado da masana’antu 14.”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel