Lai Mohammed ya saba umurni na yayin da mayar wa Obasanjo martani - Buhari

Lai Mohammed ya saba umurni na yayin da mayar wa Obasanjo martani - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya hana mashawarcinsa na musamman kan kafafen yadda labarai Femi Adesina mayar da martani ga wasikar tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo saboda ba sa'an sa bane.

Shugaba Buhari ya yi wannan bayanin ne lokacin da ya ke karbar bakuncin kungiyar magoya bayansa a fadar Aso Villa da ke Abuja a daren jiya.

Buhari ya kuma ce dalili na biyu da ya sa bai mayar da martani kan wasikar ba shine saboda shi da Obasanjo dukkansu sojoji ne.

Lai Mohammed ya saba umurni na yayin da mayar wa Obasanjo martani - Buhari

Lai Mohammed ya saba umurni na yayin da mayar wa Obasanjo martani - Buhari

Duk da hakan, shugaban kasar ya ce Ministan yadda labarai da al'addu, Lai Mohammed da ya "saba wa umurnin sa" na mayar da martani ga wasikar ya cancanji yabo saboda ya yi aiki mai kyau.

KU KARANTA: Duba jerin jami'o'i mafi nagarta a Najeriya kamar yadda NUC ta fitar

Ya lura cewa Lai Mohammed ya fede wa 'yan Najeriya biri har wutsiya a kan halin da tattalin arzkin Najeriya ke ciki yayin da gwamnatinsa ta karbi mulki a shekarar 2015 da kuma kokarin da gwamnatin keyi na kawo gyra.

"Ya ce dole in bar shi ya mayar da martani; saboda na san cewa shi kwararen dan jarida ne sai na saurare shi na tambayi abinda zai fada.

"Sai ya ce zai tunatar da yan Najeriya halin da muka tsinci kan lokacin da muka karba mulki a shekarar 2015 da halin da muke ciki a yanzu da kuma abubuwan da muka aikata da kudaden da ke hannun mu.

"Na kuma fahimci cewa ya yi aiki mai kyau saboda mutane da dama sun kira ni a way suna shaida min cewa Lai Mohammed ya mayar da martani yadda ya dace."

Shugaban kasan ya mika godiyarsa ga tawagar magoya bayansa bisa ziyarar da suka kawo masa musamman a irin wannan wata mai albarka tare da yabon da suka yi masa game da nasarorin da ya samu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel