Atiku da Jam'iyyar PDP sun yi Gargaɗi akan ɗaure Obasanjo

Atiku da Jam'iyyar PDP sun yi Gargaɗi akan ɗaure Obasanjo

Jam'iyyar adawa ta PDP da kuma tsohon Mataimakin shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar, sun yi gargaɗi ga gwamnatin jam'iyyar APC akan ɗaure tsohon shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo.

Cikin wata sanarwa a ranar Juma'ar da ta gabata, jam'iyyar ta bayyana mamakin ta dangane da kiran tsohon shugaban kasar na cewar gwamnatin shugaban Kasa Muhammadu Buhari na shirya tuggu na kazafin ɗora ma sa laifuka tare da yi ma sa ɗauri na din-din-din.

Sanarwar ta bayyana cewa, koken tsohon shugaban kasa na cewar gwamnatin shugaba Buhari na shirin ɗaure shi batu ne mai ban tsoro da tashin hankali ga al'ummar kasar nan wanda hakan yake nuna cewar kasar nan ta zamto ci da karfi.

Jam'iyyar take cewa, wannan lamari ya haskaka barazana gami da hatsarin dake tattare da duk wani wanda bambanta ra'ayin sa da kudirin shugaba Buhari na sake tsayawa takarar a zaben 2019.

Atiku da Jam'iyyar PDP sun yi Gargaɗi akan ɗaure Obasanjo

Atiku da Jam'iyyar PDP sun yi Gargaɗi akan ɗaure Obasanjo

Ta kara da cewa, ba bu wata barazana ko tozarci gami da ɗauri ba tare da hakki ba da za su sanya 'yan Najeriya su juya baya da barin watsar da mulkin kama karya na jam'iyyar APC a zaben 2019.

A yayin haka kuma, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, cikin wata sanarwa ya shawarci gwamnatin Buhari da makarrabanta akan daukar matakai da za su dakile tunzarar al'umma bayan wanda aka riga da yi.

KARANTA KUMA: Rundunar Sojin 'Kasa ta Sheke wasu 'Yan Ta'adda 5 a Jihar Zamfara

Atiku ya ke cewa, ya na rokon shugaba Buhari akan kauracewa yanke wannan mummunan hukunci a kasar nan.

Ya kara da cewa, nasabar Obasanjo a kasar nan na da matukar muhimmanci musamman ga ta fuskar Dimokuradiyya wadda manufar kowace gwamnati shine tabbatar da an sharbi wannan romo na Dimokuradiyya cikin kwanciyar hankali tare da bayar da kariya ga lafiya da kuma dukiyar al'ummar ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel