Dalilin da yasa Buhari ke shirya min makirci - Obasanjo

Dalilin da yasa Buhari ke shirya min makirci - Obasanjo

A jiya ne tsohon shugaban kasan Najeiya Cif Olusegun Obasanjo ya yi ikirarin cewa gwamnatin shugaba Buhari na shirin kama shi inda ya kara da cewa tuni an rubuta sunansa cikin wadanda gwamnati ke fako saboda irin sukar da ya ke yiwa gwamnatin.

Tsohon shugabab kasar ya aike da wasika ga Buhari a watan Janairu inda ya shawarce shi da ya hakura da sake fitowa takara a 2019 kuma ya ce gwamnatinsa ba ta tabuka wa yan Najeriya wani abin a zo a gani ba.

Ya kuma sake cigaba da suka ga gwamnatin Buhari inda har ma ya yi kira ga 'yan Najeriya su juya wa Buhari baya lokacin kada kuri'a.

Dalilin da yasa Buhari ke shirya min makirci - Obasanjo

Dalilin da yasa Buhari ke shirya min makirci - Obasanjo

KU KARANTA: Soja mazan fama: Wani jarumin soja ya kwace bindiga daga hannun 'dan fashi da makami

A bangarensa, shugaba Buhari ya mayar da martani ga Obasanjo inda ya zargi shi da wadaka da kudi har $16 biliyan wanda aka ware don gyaran wutar lantarki ba tare da kwaliya ta biya kudin sabulu ba.

Obasanjo ya fitar da wata sanarwa ta bakin mai magana da yawunsa inda ya ce ya samu bayannan sirri daga kwakwarar majiya cewa gwamnati na shirya makircin yadda za'a halaka shi.

A cewar sanarwan, cikin makircin da aka shirya wa, za'a kwace masa fasfo na tafiya kasashen waje kana a jefa shi kurkuku saboda a hana shi fadin albarkacin bakinsa game da gwamnatin Buhari.

Obasanjo ya kuma yi ikirarin cewa gwamnatin Buhari na shirin umurtan hukumar EFCC ta bude bincike a kan abubuwan da ya yi lokacin mulkinsa tare da kawo shaidun karya da takardun bogi duk dai saboda a rufe bakinsa.

Sai dai Obasanjo ya ce duk wadannan barazanan ba za su hana shi cigaba da gwagwarmayar da ya ke yi don ceto al'umman Najeriya daga halin da suka shiga ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel