Yadda wata matar fasto ta halaka 'dan kishiyarta saboda abinci

Yadda wata matar fasto ta halaka 'dan kishiyarta saboda abinci

Hukumar Yan sanda na jihar Ogun ta kama wata mace mai suna Oluwabunmi Metofik bisa zarginta da laifin dukkan 'dan kishiyarta ta, Femi, mai shekaru bakwai har sai da ya mutu saboda ya ci abincin da ta ajiye ba tare da ya nemi izininta ba.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Oluwabunmi tana auren wani Fasto ne da ke zaune a jihar Oyo.

A ranar da abin ya faru, Oluwabunmi ta yiwa Femi dukka kuma tayi masa munanan rauni har sai da ya suma. An garzaya dashi zuwa wani asibitin kudi amma likitocin basu karbe su ba.

Yadda wata matar fasto ta halaka 'dan kishiyarta saboda abinci

Yadda wata matar fasto ta halaka 'dan kishiyarta saboda abinci

Sun fada mata ta tafi da Femi asibitin Koyarwa na Olabisi Onabanjo inda a nan ne aka tabbatar da cewa ya rasu.

KU KARANTA: An damke wata mahaifiya da ta kashe jaririn ta a Sakkwato

Wani mazaunin unguwar ne ya lura da irin raunin da ke jikin yaron kuma ya sanar da yan banga. Yan bangan sun tafi gidan matan inda suka kama ta suka mika wa yan sanda.

Bayan anyi mata tambayoyi, ta amsa cewa tayi masa dukka sosai wanda hakan ne ya yi sanadiyar rasuwarsa.

"Ta ce ta sayo abinci amma da ta fita dibo ruwa sai ta dawo ta lura cewa yaro ya ci abincin. Hakan yasa tayi masa dukka kamar yadda za tayi wa yaran ta. Ta amsa cewa tayi masa rauni a kansa.

Babban danta ya ce mahaifiyarsu tayi amfani da sanda da wuka wajen hukunta Femi. A halin yanzu an mika matar da mijinta hannun yan sanda domin a zurfafa bincike.

A yayin da ya ke tabbatar da afkuwar lamarin, Kakakin hukumar Yan sanda na Jihar Ogun ASP Abimbola Oyeyemi ya ce "An sanar da yan sanda afkuwar lamarin sai dai mahaifin yaron ya ce ba matar bane ta kashe shi. Ya amince ta doke yaron amma ya ce yaron dama yana fama da rashin lafiya kawai tsautsayi ne ta afku."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel