Obasanjo: Mai Laifi ne kadai zai sanya Damuwa a ransa - Gwamnatin Tarayya

Obasanjo: Mai Laifi ne kadai zai sanya Damuwa a ransa - Gwamnatin Tarayya

Mun samu rahoton cewa gwamnatin tarayya ta yi watsi da zargin tsohon shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo, da ya ce gwamnatin shugaban Kasa Muhammadu Buhari na kulle-kullen makirci na garkame shi da tuhumar ba tare da wani tushe ba.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne tsohon shugaban Kasar ya bayyana hakan da sanadin kakakin sa, Mista Kehinde Akinyemi, inda yake cewa gwamnatin shugaba Buhari na shirin amfani da takardu da shedu na karya.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin shugaba Buhari na zargin tsohon shugaban kasar da handame kudaden wutar Lantarki da suka tasar ma Dalar Amurka Biliyan 16, wanda ya yi ikirarin batarwa ba tare da hakar ta cimma ruwa ba.

Wannan lamari ya sanya gwamnatin shugaba Buhari ke shirin fara gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiyar tsohon shugaban Kasar ko kuma kishiyar hakan da ya sanya ya fara zargin za garkame tun kafin aje ko ina.

Obasanjo: Mai Laifi ne kadai zai sanya Damuwa a ransa - Gwamnatin Tarayya

Obasanjo: Mai Laifi ne kadai zai sanya Damuwa a ransa - Gwamnatin Tarayya

A yayin da gwamnatin tarayya ke mayar da martani dangane da wannan zargi na tsohon shugaban kasar, Ministan Labarai da Al'adu na Najeriya, Alhaji Lai Muhammad ya bayyana cewa wannan zargi na Obasanjo ba ya tushe matukar yana rike gaskiyar sa.

Ministan yake cewa gwamnatin shugaba Buhari na kokarin kawar da barnar da gwamnatin jam'iyyar PDP ta yi cikin kasar nan na tsawon shekaru 16 a kan karagar mulki, inda yace duk wani mai gaskiya ba zai sanya faduwar gaba a zuciyar sa ba.

KARANTA KUMA: Tsautsayi: Dakarun Soji Kasa sun salwantar da rayuwar Mai Jego, Jaririya da wasu Mutane 2 a Jihar Bayelsa

Ya ci gaba da cewa, dole ne duk wani wanda ya aikata rashin gaskiya a baya ya sanya damuwa a zuciyar sa sakamakon bincike da gwamnatin shugaba Buhari ke ci gaba da yi na kwato hakkin al'ummar kasar nan.

Ministan ya kuma bayyana mamakin sa dangane da yadda tsohon shugaban Kasar ya tayar da hankalin sa da cewar damuwa agami d faduwa gaba na tunkarar zukatan marasa gaskiya ne ya kuma jaddada cewa Obansajo na kokarin nade tabarmar sa ta kunya ne da hauka.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tsautsayi gami da karar kwana ya sanya wasu Dakarun Soji sun salwantar da rayuwar wata Jaririya, Mahaifiyar ta da kuma wasu Mutane biyu a jihar Bayelsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel