Gwamnati za ta maida Gidajen Karuwai Makarantu a Jihar Borno

Gwamnati za ta maida Gidajen Karuwai Makarantu a Jihar Borno

Da sanadin shafin jaridar The Guardian mun samu rahoton cewa, gwamnatin jihar Borno ta shirya maida Gidajen Karuwai dake Birnin Maiduguri zuwa Makarantu domin al'umma su amfana.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito, gwamnatin jihar ta kaddamar da wani Babban Kwamiti da Kwamishinan Shari'a na jihar Alhaji Kaka Shehu Lawan ke jagoranta domin kawar da Gidajen Karuwai da ake aikata Fasikanci.

Gwamnati za ta maida Gidajen Karuwai Makarantu a Jihar Borno

Gwamnati za ta maida Gidajen Karuwai Makarantu a Jihar Borno

Legit.ng ta fahimci cewa, Gwamnatin Jihar ta bayar da umarnin tarwatsa Gidajen Karuwai musamman na Galadima da ya yi kaurin suna inda za ta maida harabar sa Makarantun gwamnati a Birnin Maiduguri domin amfanar al'umma.

KARANTA KUMA: 'Daukan Aiki: Hukumar 'Yan sanda ta saki Jerin Sunayen Mutanen da suka yi Nasara

Gwamnan a yayin ziyarar gani na ido da ya kai wannan yankuna ya bayyana cewa, gwamnatin sa ta yanke wannan hukunci ne domin hakan zai taimaka matuka wajen dakile bayar da Mafaka ga Mabarnata da Miyagun Mutane.

A yayin haka kuma Gwamnan ya yabawa wannan Kwamiti sakamakon kwazon da ya gudanar na tarwatsa duk wani sanannun Gidajen Karuwai da Mashaya dake cikin garin Maiduguri.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a yau ne Hukumar 'Yan sanda ta fitar da jerin sunayen Mutanen da suka taki nasara ta daukar aiki inda ta wallafa a shafin ta na Yanar Gizo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel