Osinbajo ya Ziyarci Gwamna Ajimobi a Jihar Oyo, Sun Shige Bayan Labule

Osinbajo ya Ziyarci Gwamna Ajimobi a Jihar Oyo, Sun Shige Bayan Labule

A ranar Juma'ar da ta gabata ne Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ziyarci gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, a fadar gwamnatin sa ta Sakateriyar Agodi dake babban Birnin Ibadan a jihar ta Oyo.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Osinbajo ya gudanar da ganawar sirrance tare da Gwamnan a fadar sa dake birnin Ibadan.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Osinbajo ya sauka a fadar Gwamnan nan ne da misalin karfe 3.20 na yammacin ranar yau ta Juma'a.

Osinbajo ya Ziyarci Gwamna Ajimobi a Jihar Oyo, Sun Shige Bayan Labule

Osinbajo ya Ziyarci Gwamna Ajimobi a Jihar Oyo, Sun Shige Bayan Labule
Source: Depositphotos

Rahotanni sun bayyana cewa, Osinbajo ya iso fadar gwamnan tare da 'yan rakiyar sa da suka hadar da; Kwamishinan 'yan sanda na Jihar, Mista Abiodun Odude da kuma shugaban hukumar DSS na jihar, Mista Abdullahi Kure.

KARANTA KUMA: Ministan Sadarwa ya zargi Gwamna Ajimobi da Laifin rincaɓewar Jam'iyyar APC a Jihar Oyo

Sai dai kawowa yanzu ba bu wanda ke da masaniyar abinda da shugabanni biyun suka tattauna cikin ganawar ta su ta sirrance yayin da suka ƙi yarda su gana da manema labarai.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya tare da shafin jaridar The Nation sun ruwaito cewa, bayan ganawar ta su gwamnan tare da mataimakin shugaban kasar sun kuma kama gaban su zuwa wani wuri da har yanzu ba a fayyace ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel