Masu tafiyan kafa da sauri-sauri sun fi tsawon rai - Bincike

Masu tafiyan kafa da sauri-sauri sun fi tsawon rai - Bincike

Rahotanni sun kawo cewa wani sabon bincike da aka gudanar a kasar Ingila ya nuna cewa nasabar dake tsakanin tafiyan kafa fa sauri-sauri da kuma tsawon rai.

Masana a kasashen Burtaniya da na Ostireliya sun bayyana cewa, mafi akasarin masu tafiya a kafa cikin gaggawa basa kamuwa da ciwon zuciya.

Ana ganin mafi akasarin mutane masu sama da shekaru 60 dake mutuwa sanadiyan ciwon zuciya ya ragu da 53% sakamakon wannan dabara.

Masu bincike sun gano cewa,tafiya da kafa da sauri tsawon awanni 5 zuwa 7 sun isa matuka gaya ga masu bukatar su rayu cikin lafiya.

Masu tafiyan kafa da sauri-sauri sun fi tsawon rai - Bincike

Masu tafiyan kafa da sauri-sauri sun fi tsawon rai - Bincike

Manufar wannan tafiyar ita ce, bai wa zuciya damar bugawa da gaggawa,shi yasa kamata yayi a dinka takawa da sauri ta yadda za a yi kankanuwar zufa.

KU KARANTA KUMA: Tsintsiya madaurinki daya: An gano Dolapo Osinbajo tana taya Aisha Buhari daurin dankwali

Masanar Burtaniyar sun sanar da cewa, motsa jiki tsawon dakiku 30 a kowace rana da kuma cin lafiyayyen abinci, na tsawaita raywuwar mutum da shekaru 10.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Domin samun ingantattun labarai ku bide mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel