Yanzu Yanzu: Babu hutu a ranar 12 ga wata Yuni – Gwamnatin tarayya

Yanzu Yanzu: Babu hutu a ranar 12 ga wata Yuni – Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da cewa babu hutun aiki a ranar 12 ga watan Yuni, 2018.

A wata sanarwa da ta saki ta shafin @AsoRock, a ranar Juma’a 8 ga watan Yuni, gwamnatin tarayya tayi bayanin cewa umurnin shugaban kasar na nufin cewa “12 ga watan Yuni” zai maye gurbin 29 ga watan Yuni anan gaba a matsayin ranar bikin damokradiyyar Najeriya."

A cewar gwamnatin, hakan na nufin 2018 baya daga ikin shekarar da za’a yi bikin damokradiyya a ranar 12 ga watan Yuni.

Ga sakon a kasa:

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na shirya makirci don a kama ni akan tuhume-tuhume na karya – Obasanjo ya nemi dauki

A baya Legit.ng ta rahoto cewa majalisar dattawa ta yi adawa da batun June 12 da Buhari ya kaddamar a matsayin ranar damokradiyya, tace har yanzu ranar 29 ga watan Mayu ce ranar rantsar da sabbin shugabanni.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Domin samun ingantattun labarai ku bide mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel