Wani mutum mai shekaru 37 ya yanka mahaifiyarsa akan dukiyar gadon da mahaifinsa ya bari

Wani mutum mai shekaru 37 ya yanka mahaifiyarsa akan dukiyar gadon da mahaifinsa ya bari

Rahotanni sun kawo cewa wani mutumi mai shekaru 37 a duniya mai suna Nurudeen ya hallaka mahaifiyarsa mai shekaru 65.

Matashin dai ya kashe mahaifiyar tasa ne ta hanyar yi mata yankan rago a ranar Larabar da ta gabata.

Lamarin ya afku ne a yankin Mushin, jihar Legas, bayan ya zargi uwar tasa da yin kaka-gida akan gadonsa da mahaifinsa ya mutu ya bar masa.

A ranar da abun ya faru, Nuruddeen ya ya samu sabani da mahaifiyar kan cewa llalai sai dai ta bashi gadonsa, hakan ya haddasa rikici, nan take Nuruddeen ya dauki wuka ya daba wa mahaifiyar tasa a ciki, bayan ta fadi kuma ya yanka makogwaronta kamar dai yadda ake yanka rago.

Wani mutum mai shekaru 37 ya yanka mahaifiyarsa akan dukiyar gadon da mahaifinsa ya bari

Wani mutum mai shekaru 37 ya yanka mahaifiyarsa akan dukiyar gadon da mahaifinsa ya bari

Wata shaidar gani da ido da aka bayyana sunanta da Iya Bose, ta bayyana cewa ta jiyosu suna cacar baki, amma ba ta yi zaton har lamarin zai kai ga kisan kai ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na shirya makirci don a kama ni akan tuhume-tuhume na karya – Obasanjo ya nemi dauki

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta bakin kakakinta, Sufurentandan ‘yan sanda Chike Oti ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta kara da cewa tuni dai aka kama Nuruddeen aka mika shi ga sashen kisan kai na rundunar da ke a yankin Yaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Domin samun ingantattun labarai ku bide mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel