Yanzu Yanzu: Buhari na shirya makirci don a kama ni akan tuhume-tuhume na karya – Obasanjo ya nemi dauki

Yanzu Yanzu: Buhari na shirya makirci don a kama ni akan tuhume-tuhume na karya – Obasanjo ya nemi dauki

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo yayi zargin cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kulla wani makirci domin tsare shi har sai illa mashaa Allah akan tuhume-tuhume mara tushe.

Premium Times ta rahoto cewa Obasanjo ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya saki ta hannun kakakinsa, Kehinde Akinyemi a ranar Juma’a, 8 ga watan Yuni.

Yayi ikirarin cewa gwamnatin shugaba Buhari shirin yin amfani da takardun karya da shedu na karya a kansa.

Wannan ikirari na zuwa ne yan makonni bayan musayar yawu da akayi tsakanin shugabannin biyu, wadanda suka raba jiha bayan Obasanjo ya zargi shugaba Buhari da rashawa sannan kuma ya shawarce shi da kada ya sake neman takara.

Yanzu Yanzu: Buhari na shirya makirci don a kama ni akan tuhume-tuhume na karya – Obasanjo ya nemi dauki

Yanzu Yanzu: Buhari na shirya makirci don a kama ni akan tuhume-tuhume na karya – Obasanjo ya nemi dauki

Buhari ya maida masa da martani ta hanyar zarginsa da wawushe dala biliyan 16 na aikin wutar lantarki. Inda Obasanjo ya maida martani a matsayin ikirarin rashin sani.

KU KARANTA KUMA: Mazan jiya: A yau marigayi Janar Sani Abacha ya cika shekaru 20 da mutuwa

Da yake magana ta hannun hadiminsa a ranar Juma’a, tsohon shugaban kasar yace shirin sa shi yin shiru ne yasa aka shirya makirci wanda hukumar EFCC ta sake bude shafin bincike a ayyukan gwamnatinsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Domin samun ingantattun labarai ku bide mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel