Ministan Sadarwa ya zargi Gwamna Ajimobi da Laifin rincaɓewar Jam'iyyar APC a Jihar Oyo

Ministan Sadarwa ya zargi Gwamna Ajimobi da Laifin rincaɓewar Jam'iyyar APC a Jihar Oyo

Wani Ministan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zargo gwamna Abiola Ajimobi da sanya rudani da rincabewar Jam'iyyar APC a jihar sa.

Ministan na sadawarwa, Adebayo Shittu, ya zargi gwamnan Jihar Oyo da gazawar kwana-kwanan da ta mamaye Jam'iyyar APC a jihar Oyo.

Cikin wata rubutacciyar wasika da Ministan ya aikawa shugaban jam'iyyar na kasa, Cif John Odigie-Oyegun, ya bayyana cewa matakan tafi da ayyuka da gwamna Ajimobi ke dabbakawa a jihar sa ke janyo kasawar jam'iyyar su ta APC.

Mista Shittu yake cewa, hawan kawara da gwamna Ajimobi yake yiwa Dimokuradiyya ya janyo duk wata rincabewa cikin jam'iyyar APC, wanda idan da hakan ta kasance da bai samu nasarar lashe zaben jihar a karo na biyu.

Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu, ya zargi Gwamna Ajimobi da Laifin rincaɓewar Jam'iyyar APC a Jihar Oyo

Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu, ya zargi Gwamna Ajimobi da Laifin rincaɓewar Jam'iyyar APC a Jihar Oyo

Legit.ng ta fahimci cewa Ministan ya zargi gwamna Ajimobi da gudanar da mulkin mallaka a sassa daban-daban cikin jam'iyyar a jihar sa a madadin bayar da dama ga sauran mambobin ta su bayyana ra'ayoyin su na tafi da jam'iyyar.

KARANTA KUMA: Gwamnan Jihar Neja, Sani Bello, ya karbi Bashin N3.2bn daga Bankin Zenith

Ministan ya kuma zargi gwamna Ajimobi da nuna wariya wajen bayar da kulawa ta musamman ga mambobin wasu jam'iyyun yayin nadin mukaman gwamnati a jihar ta Oyo.

Sai dai Kakakin jam'iyyar na jihar, Abdulazeez Olatunde, ya mayar da martani da cewar irin yankan kauna sabo ne Ministan.

Ya kara da cewa, ba bu wata rawa da Ministan ya taka wajen nasarar lashen zaben gwamnan jihar a karo na biyu.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya karbi bashin N3.2bn daga bankin Zenith domin gudanar da wasu muhimman ayyuka a jihar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel