An damko fursunoni 55 daga cikin wanda suka tsere daga gidan yarin Minna

An damko fursunoni 55 daga cikin wanda suka tsere daga gidan yarin Minna

- Shugaban hukumar kula da gidajen yari na kasa ya ce gwamnatin tarayya tana gab da magance karancin jami'ai da hukumar ke fama dashi

- Ya yi kira ga manyan jami'an hukumar su cigaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda doka ta tanada

- Ya kuma ce hukumar ta yi nasarar kamo fursunoni 55 daga cikin 210 da suka gudu daga gidan yarin

A cikin matakan da ta dauka kan fursunonin da suka tsere daga sabon gidan yarin Minna da ke jihar Neja, hukumar kula da gidajen yari na kasa (NPS) ta kafa kwamiti da zai gano musababin dalilin da ya janyo afkuwar lamarin.

Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban hukumar kula da gidajen yarin na kasa, Ja'afaru Ahmed ne ya bayyana kafa kwamitin yayin da ya ke ganawa da wasu manyan jami'an hukumar a wata taron gagawa da ya kira a ranar Alhamis a Abuja.

An damko fursunoni 55 daga cikin wanda suka tsere daga gidan yarin Minna

An damko fursunoni 55 daga cikin wanda suka tsere daga gidan yarin Minna

KU KARANTA: Dakarun soji sunyi wa 'yan bindiga diran mikiya a Zamfara

Ahmed ya kuma ce an kama 55 daga cikin fursunoni 210 da suka gudu.

Ya ce ana kara mayar da hankali wajen ganin an damko dukkan fursunonin da suka gudu.

Ahmed ya ce: "Duk da cewa daga waje aka shiryo harin, ina ganin akwai bukatar mu sake duba zuwa ga kanmu don ganin cewa sun sauke nauyin da ke kanmu na tabbatar da tsaron lafiyan fursunonin da ke karkashinmu a kowanne lokaci."

Ya ce gwamnatin tarayya ta fara aiki don ganin ta magance matsalar karancin ma'aikata da hukumar ke fama da shi.

"Ana magance matsalar karancin ma'aikata saboda hukumar ta fara aikin tantance sabbin ma'aikatan hukumar. Ya zama dole mu cigaba da gamsar da gwamnatin tarayya ta hanyar yin aikin mu yadda ya kamata don a kara sakar mana kudaden aiki," inji Ahmed.

Ya kuma bukaci manyan ma'aikatan hukumar su dage wajen ganin suna gudanar da ayyukansu kamar yadda ya kamata.

Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau ya ziyarci gidan yarin na Minna bayan afkuwar lamarin. Mutane biyu sun rasa rayyukansu sakamakon harin gidan yarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel