Bahallatsar majalisar Dattawa da Yansanda: El-Rufai ya yaba da aikin Sufetan Yansanda

Bahallatsar majalisar Dattawa da Yansanda: El-Rufai ya yaba da aikin Sufetan Yansanda

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya jinjina ma aikin da babban sufetan Yansandan Najeriya, Ibrahim Idris Kpotun yake yi, musamman dangane da kokarin magance tsaro da tashe tashen hankula.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Nasir ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Yuni a yayin taron wa’azin watan Ramadana da ministan watsa labaru da al’adun gargajiya, Lai Muhammed ya shirya a mahaifarsa dake garin Oro jihar Kwara.

KU KARANTA: Wata daliba a jihar Sakkwato ta kashe jaririnta dan gaba da fatiha

Gwamnan ya bayyana haka Sufetan a matsayin jajirtaccen mutum wanda ya san ya kamata, kuma kwararre wajen sanin makaman aiki, sai dai El-rufai na wannan batu ne a daidai lokacin da majalisar dokokin Najeriya ta nuna rashin amincewarta da Sufetan, inda tace ya gaza.

Bahallatsar majalisar Dattawa da Yansanda: El-Rufai ya yaba da aikin Sufetan Yansanda

El-Rufai a Kwara

A wani zama na gaggawa da yan majalisun suka yi, sun nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsige IG Idris daga mukamin babban sufetan Yansanda saboda rashim mutunta majalisar, tabarbarewar tsaro a kasar, shafa ma shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki kashin kaza game da wasu yan fashi da kuma afka ma majalisa da aka yi aka sace sandan ikon ta.

“Ina mika godiyata ga babban limami game da addu’ar zaman lafiya da yayi ma kasarmu, da shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma babban sufetan Yansandan Najeriya jajirtaccen mutum dake aiki ba dare ba rana, har ma da ministan watsa labaru, Allah ya karba.” Inji El-Rufai

Bahallatsar majalisar Dattawa da Yansanda: El-Rufai ya yaba da aikin Sufetan Yansanda

El-Rufai a Kwara

A nasa jawabin, Minista Lai ya yaba ma El-Rufai da amsa wannan gayyata, inda ya bayyana shi a matsayin mutumin da baya nuna bambancin addini ko na kabila, sa’annan ya bayyana mutanen garin Oro a matsayin mutane ne masu kaunar juna, saboa a cewarsa yawancin wadanda suka halarci taron Kiristoci ne yan kabilar Oro, haka zalika an gudanar da wasu wa’azukan ma a harabar coci coci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel