Shugaba Buhari: Matasa ku cigaba da hakuri muna nan muna iya bakin kokarin mu don ganin mun dawwamar da cigaba a rayuwar ku

Shugaba Buhari: Matasa ku cigaba da hakuri muna nan muna iya bakin kokarin mu don ganin mun dawwamar da cigaba a rayuwar ku

- A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewar gwamnatinsa tana yi iya bakin kokarin ta wurin ganin ta kawo cigaba mai dorewa a kasar nan

- Shugaban kasar ya tabbatar da hakan ne a jiya lokacin daya karbi bakuncin kungiyar mawaka da matasan Najeriya, wadanda suka je fadar shi domin yin buda baki a babban birnin tarayya.

Shugaba Buhari: Matasa ku cigaba da hakuri muna nan muna iya bakin kokarin mu don ganin mun dawwamar da cigaba a rayuwar ku

Shugaba Buhari: Matasa ku cigaba da hakuri muna nan muna iya bakin kokarin mu don ganin mun dawwamar da cigaba a rayuwar ku

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewar gwamnatinsa tana yi iya bakin kokarin ta wurin ganin ta kawo cigaba mai dorewa a kasar nan. Shugaban kasar ya tabbatar da hakan a jiya lokacin da karbi bakuncin kungiyar mawaka da matasan Najeriya, wadanda suka je fadar shi domin yin buda baki a babban birnin tarayya.

DUBA WANNAN: Duniya ina zaki damu: An kama wasu daliban sakandare sun hada kungiyar asiri, da kuma laifin sace - sace

Ya bayyana cewar dokar kasa ta bashi damar yin aiki tukuru domin tabbatar da rayuwar kowanne dan Najeriya ta inganta. Saboda haka nema, shugaban kasar yayi alkawarin cewar gwamnatin sa zata cigaba da yin iya bakin kokarin ta wurin ganin ta kawo hanyoyin cigaba ga matasa ta kowacce hanya.

Sannan shugaban kasar ya sake yiwa jama'a alkarin cewar gwamnatinsa zata cigaba da bawa matasa goyon baya akan sana'o'in su, domin ganin sun dogara da kansu.

Mista Kunle Afolayon, wanda yayi magana a maimakon mawakan, ya yabawa gwamnatin shugaba Buharin akan kokarin da take na ganin ta kawo cigaba ga al'ummar Najeriya.

A karshe kuma yayi alkawarin cewar zasu yi iya bakin kokarin su wurin ganin sun taya shugaban kasar yakin neman zabe, domin ganin cewar gwamnatin ta samu isasshen lokaci ta cika alkawuran data dauka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel