Majalisar dokoki bata yi barazanar tsige shugaban kasa ba – Ministan Buhari

Majalisar dokoki bata yi barazanar tsige shugaban kasa ba – Ministan Buhari

Akan fassarar da mutane suka ba sharuda 12 da majalisar dokoki ta gindayawa shugaban kasa Muhammadu Buhari, ministan bayanai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa babu ta wata hanya da yan majalisan suka yi barazanar tsige shugaban kasar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wani dan majalisa yayi zargin cewa an fara tattara sa hannu domin tsige shugaban kasar a ranar Talata da ta gabata.

Da yake amsa tambayoyi daga yan jarida a filin jirgin sama na Ilorin bayan taron darasin Ramadan karo na 11 a garinsa na Oro a ranar Alhamis, ministan ya bayyana cewa baida masaniya akan ko wani barazanar tsigewa da majalisar dokoki ta shirya yi.

Majalisar dokoki bata yi barazanar tsige shugaban kasa ba – Ministan Buhari

Majalisar dokoki bata yi barazanar tsige shugaban kasa ba – Ministan Buhari
Source: Twitter

Idan zaku tuna yan majalisan sun bayyana cewa zasu yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya basu idan har shugaban kasar ya gaza magance lamuran da suka zanta akai a zaman da sukayi a ranar Talata.

KU KARANTA KUMA: Masu laifin da basu da gata rundunar yan sandan Najeriya ke kamawa - Falana

Daga cikin abubuwan da yan majalisan suka bukaci Buhari yayi sune, dakatar da kashe-kashe a kasar, dakatar da cin zarafin abokan hamayya, hukunta wadanda suka kai hari majalisa suka sace sadar iko da kuma nuna rashin amincewa da sufeto janar na yan sanda.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel