Dubi irin cigaban da ma'aikatar Sufuri zata kawowa matasan Najeriya

Dubi irin cigaban da ma'aikatar Sufuri zata kawowa matasan Najeriya

Sakataren Gwamnatin tarayya, Chinyeaka Ohaa, yace titin jirgin kasa da zai fara aiki a Abuja, zai habaka tattalin arziki ta hanyar bunkasa hannayen jari da samar da aiyukan yi

Dubi irin cigaban da ma'aikatar Sufuri zata kawowa matasan Najeriya

Dubi irin cigaban da ma'aikatar Sufuri zata kawowa matasan Najeriya

Sakataren Gwamnatin tarayya, Chinyeaka Ohaa, yace titin jirgin kasa da zai fara aiki a Abuja, zai habaka tattalin arziki ta hanyar bunkasa hannayen jari da samar da aiyukan yi.

Ohaa ya bada tabbacin hakan a ranar Alhamis dinnan a babban birnin tarayya, inda ya jagoranci daraktoci da jami'an gwamnati gurin duba titin jirgin kasan a Abuja mai tsawon kilomita 78.

DUBA WANNAN: Dubi irin kudaden da Amurka ta bawa Najeriya tallafi

Ya kara tabbatar da cewa hukumar tasu ta rubuta takarda zuwa ga shugaban kasa akan ranar kaddamar da sabon titin jirgin.

"Amfanin sabon titin jirgin ya hada da samar da aiyukan yi ga al'umma har guda 20,000 da kuma habaka tattalin arzikin kasar."

Yace an fara aikin titin jirgin kasan tun a shekarar 2009 wanda zai kawo sassaucin cunkoson ababen hawa da ake samu a titunan motoci a babban birnin tarayya.

Ohaa ya kara da cewa an samar da duk abubuwan more rayuwa da kuma mutanen da zasu tabbatar da kaddamarwa ya tafi dai dai.

Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa aikin ya fara daga Metro station zuwa Airport Terminal station zuwa Kubwa station ya nuna cewa kashi 98 a cikin dari na aikin ya kammala.

Sakataren Gwamnatin wanda ya kwatanta aikin da sabon salo a Africa, ya kara da cewa, yana farin ciki da aiyukan da yaga sun kammala.

Ohaa yace shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministan tarayya sun nuna bajintar su gurin tabbatar da samuwar titin jirgin kasan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel