Masu laifin da basu da gata rundunar yan sandan Najeriya ke kamawa - Falana

Masu laifin da basu da gata rundunar yan sandan Najeriya ke kamawa - Falana

Babban lauya kuma mai kare hakkin dan adam, Mista Femi Falana (SAN), ya caccaki nuna masu laifi da yan sanda suka yi a kafofin watsa labarai ya bayyana hakan a matsayin ba bisa ka’ida ba.

Da yake agana akan lamarin Falana yace talakawa da marasa gata kadai ne masu aikata laifi, inda yace hakan na iya lalata tsarin adalci.

“Ba ku gurfanar da manyan mutane, ba ku gurfanar da manyan yan siyasa. Talakawa kawai kuke gurfanarwa,” inji shi.

Masu laifin da basu da gata rundunar yan sandan Najeriya ke kamawa - Falana

Masu laifin da basu da gata rundunar yan sandan Najeriya ke kamawa - Falana

Falana yayi sharhi akan hukunci wata kotun koli da ta dakatar da tsawaita shari’an masu laifi, inda ta bayyana tsawaitawar a matsayin makiri da wasu lauya kanyi don jinkirta shari’an masu laifi dace da karfi da baki a kasa.

KU KARANTA KUMA: Yan majalisa ba za su iya razana shugaba Buhari ba - Malami

“Lamari ne na matsayi, ba’a ba talakawa dake kotun majistare wannan damar,” cewarsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel