Karamma Abiola da Mukamin GCFR ya tabbatar da shi ya Lashe Zaben Shugaban Kasa na 1993 - Tinubu

Karamma Abiola da Mukamin GCFR ya tabbatar da shi ya Lashe Zaben Shugaban Kasa na 1993 - Tinubu

Kanwa Uwar gamin matsaloli kuma babban jagora na Jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya fashin baki dangane da karramacin GCFR da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yiwa Marigayi Cif Moshood K. Abiola a ranar Larabar da ta gabata.

Jagoran na jam'iyyar APC ya bayyana cewa ko shakka babu wannan karramci na GCFR ya tabbatar da cewa Marigayi Abiola shi ya lashe zaben shugaban Kasae najeriya da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin 1993.

Tinubu ya yi wannan fashin baki ne yayin ganawa da 'yan jarida na kamfanin Dillancin Labarai a jihar sa ta Legas da sanadin Kakakin sa, Mista Tunde Rahman.

Cikin jawaban na Tinubu a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana cewa, karrama Abiola da mukamin GCFR ya tabbata cewa shi ya kamata a bai wa damar shugabantar kasar nan ta Najeriya bayan gudanar da tsarkaken zabe na gaskiya da adalci kamar yadda mafi akasarin al'ummar kasar nan suka amince.

Karamma Abiola da Mukamin GCFR ya tabbatar da shi ya Lashe Zaben Shugaban Kasa na 1993 - Tinubu

Karamma Abiola da Mukamin GCFR ya tabbatar da shi ya Lashe Zaben Shugaban Kasa na 1993 - Tinubu

Legit.ng ta fahimci cewa, Marigayi Abiola bai samu wannan dama ba sakamakon tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, da ya soke sakamakon zaben bisa wasu dalilain da ya shimfida a wancan lokaci.

A ranar Larabar da ta gabata ne shugaba Buhari ya kaddamar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin sabuwar ranar Dimokuradiyya ta Kasar Najeriya da za a fara dabbaka wa a shekarar 2019.

KARANTA KUMA: Rayuka 2 sun salwanta a wani Rikicin 'Kungiyoyin Asiri da ya afku a Jihar Ebonyi

Shugaba Buhari ya kuma karrama abokin takarar Abiola, Ambasada Baba Kingibe da kuma wani babban lauya mai kare hakkin dan Adam, Gani Fayehinmi da mukaman GCON (Grand Commander of the Niger).

Tinubu yake cewa wannan muhimmiyar rawa da shugaba Buhari ya taka ta zamto abin alfahari a Najeriya da kuma tabbatar a ci gaba da sharbar romon Dimokuradiyya a cikin ta sakamakon gyara da ya yiwa kura-kuran da suka afku a baya.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan sabuwar ranar Dimokuradiyya ta 12 ga watan Yuni za ta maye gurbin ranar 29 ga watan Mayu da aka saba gudanar wa a kasar nan cikin tsawon lokutan da suka shude.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, adawa a tsakanin wasu kungiyoyin asiri ta yi sanadiyar salwantar rayukan mutane biyu a jihar Ebonyi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel