Gwamnatin Buhari ta jaza kara farashin kudin giya da taba da kaso 15 cikin 100

Gwamnatin Buhari ta jaza kara farashin kudin giya da taba da kaso 15 cikin 100

Biyo bayan matakan da gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta dauka na kara haraji a kan giya da taba a kasar nan tun daga ranar 1 ga watan Yunin da ta gabata, hakan ya tilastawa kamfanonin da ke sayar da kayayyakin kara farashin shu da akalla kaso 15 cikin 100.

Wannan ne ma ya sa shugaban wani kamfanin dake sayar da giya a garin Legas da ya bukaci a sakaya sunan sa ya bayyana cewa tuni kamfanin su yayi kwaskwarima a farashin giyar su inda kiret yanzu ya koma Naira dubu 3 da dari biyar sabanin Naira dubu 3 da yake a da.

Gwamnatin Buhari ta jaza kara farashin kudin giya da taba da kaso 15 cikin 100

Gwamnatin Buhari ta jaza kara farashin kudin giya da taba da kaso 15 cikin 100

KU KARANTA: Najeriya za ta shiga matsala idan aka tsige Buhari

A wani labarin kuma, Kasar Austria dake a yammacin duniya ta sanar da kudurin ta na rufe wasu masallatai har bakwai da tace tana zargin suna karbar kudaden gudanarwar su daga kasashen waje tare kuma da korari wasu limaman masallatan kasar da dama.

Shugaban kasar ta Austria ne dai mai suna Sebastian Kurz ya sanar da kudurin gwamnatin da yake jagoranta a ranar Juma'ar da ta gabata inda ya kara da cewa za su dauki matakin ne domin tsarkake harkokin addinai a kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel