Cakwakiyar zabe: Kotu a Najeriya ta rufe asusun ajiya na INEC da Naira biliyan 34

Cakwakiyar zabe: Kotu a Najeriya ta rufe asusun ajiya na INEC da Naira biliyan 34

Yanzu haka dai ana zaman dar-dar ne a hukumar nan dake da alhakin gudanar da zabukan kasa ta tarayyar Najeriya watau Independent National Electoral Commission (INEC) sakamakon wata cakwakiya da ta ke neman kunno kai.

Kamar dai yadda muka samu, wata kotun tarayya ce a baya ta bayar da umurni ga bankunan kasar nan da su daskarar da makudan kudaden hukumar da suka kai akalla Naira biliyan 34 dake cikin asusun ta.

Cakwakiyar zabe: Kotu a Najeriya ta rufe asusun ajiya na INEC da Naira biliyan 34

Cakwakiyar zabe: Kotu a Najeriya ta rufe asusun ajiya na INEC da Naira biliyan 34

KU KARANTA: An ba Buhari kyautar motoci 2

Legit.ng ta samu cewa wannan dai ba karamin nakasu ne ba ga hukumar ta Independent National Electoral Commission (INEC) musamman ma yanzu da take shirye-shiryen gudanar da zabukan gwamnoni a jahohin Ekiti da Osun.

A wani labarin, Jami'an hana fasa kwauri na Najeriya da aka fi sani da kwastam watau Nigeria Customs Service (NCS) a turance sun kafa tarihi, yayin da suka tara kudaden da ba'a taba tarama gwamnatin tarayya ba a wata daya na Naira biliyan 100.1 a watan Mayun da ya gabata.

Ganin namijin kokarin da suka yi ne ma kuma ya sa jami'an suka kara mika kokon barar su ga gwamnatin tarayya da ta duba girman Allah ta kara masu albashi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel