Saraki da sauran 'yan majalisar dattawa ba su kauna ta - IGP Idris

Saraki da sauran 'yan majalisar dattawa ba su kauna ta - IGP Idris

- Sifeta Janar Yan sanda, Ibrahim Idris ya yi ikirarin cewa majalisar dattawa da Bukola Saraki na nuna masa kiyaya da tsana

- Sifetan Yan sandan ya fadi hakan ne a wata kara da ya shigar a kotun Abuja inda ya ke bukatar kotun ta warware ayyana shi a matsayin makiyin demokradiyya da majalisar ta yi

- Sifeta Idris kuma ya roki alfarma a wajen kotun na cewa ba zai samu damar bayyana a kotun da kansa ba yayin shari'ar

Sifeta Janar na Yan sandan Najeriya, Mista Ibrahim Idris ya shigar da kara a babban kotun Abuja inda ya ke bukatar kotun ta soke ayyana shi a matsayin "makiyin demokradiyya kuma wanda bai cancanta ya rike wata mukami a Najeriya ko kasashen waje" da majalisar tarayya da zartar a kansa a ranar 9 ga watan Mayu.

Saraki da sauran 'yan majalisar dattawa ba su kauna ta - IGP Idris

Saraki da sauran 'yan majalisar dattawa ba su kauna ta - IGP Idris

A takardan da ya shigar wa kotun don kallubalantar matakin da majalisar ta sauka a kansa, Idris ya yi ikirarin cewa 'Yan majalisar dattawan da Bukola Saraki sun dauki wannan matakin a kansa ne kawai saboda "tsabar kiyaya a fili da suke nuna masa."

KU KARANTA: Dakarun soji sunyi wa 'yan bindiga diran mikiya a Zamfara

Lauyan IGP Idris, Dakta Alex Izinyon (SAN) wanda ya bayyana a gaban Jastis John Tsoho a yau Alhamis ya roki kotun ta yi bita a kan abubuwan da suka faru gabanin matakin da majalisar dattawan ta dauka a kan sifetan Yan sandan kuma ya shigar da bukata cigaba da shari'ar ba tare da Sifeta Idris ya hallarci kotun ba.

Bayan ya duba takardun da lauyan Sufetan Yan sandan ya gabatar, Jastis Tsoho ya gamsu cewa Sifetan Yan sandan ya nuna damuwa a kan abubuwan da ke faruwa kuma ya ce amince da bukatar da cigaba da shari'ar ba tare da Sifetan ya bayyana a kotun ba.

Jastis Tsoho kuma ya kara da cewa kotun za ta sanar da majalisar dattawar da Bukola Saraki ta hanyar aikewa akawun majalisar wasika.

Justice Tsoho ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Yuli na shekarar 2018.

Wannan dai shine karo na biyu da majalisar dattawan ke fafatawa da Sufetan yan sanda a kotu, a wancan lokacin majalisar ta shigar da kara ne saboda Sifetan ya ki bayyana da kansa don amsa tambayoyi a kan Sanata Dino Melaye da kuma sauran kallubalen tsaro da ke adabar kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel