Shugaban Majalisar Dattawa Saraki ya amsa tambayoyi a gaban ‘Yan Sanda

Shugaban Majalisar Dattawa Saraki ya amsa tambayoyi a gaban ‘Yan Sanda

- Bukola Saraki ya hallara gaban ‘Yan Sanda domin amsa kiran da aka yi masa

- Ana zargin cewa Saraki yana cikin masu taimakawa masu fashi a Jihar Kwara

- Bukola Saraki dai yace Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya ne ke neman sa da sharri

Mun samu labari cewa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki ya mikan kan sa gaban Rundunar ‘Yan Sandan Kasar game da binciken sa da ake yi kan wani fashi da aka yi a Jihar Kwara.

Shugaban Majalisar Dattawa Saraki ya amsa tambayoyi a gaban ‘Yan Sanda

Bukola Saraki ya je gaban ofishin ‘Yan Sanda jiya

A jiya ne dai tsohon Gwamnan Kwara kuma Sanata a yanzu Bukola Saraki ya tashi ta-ka-nas har gaban Jami’an ‘Yan Sandan Kasar domin amsa gayyatar da aka yi masa na zargin taimakawa wasu da su kayi fashi da makami kwanaki a Garin Offa.

KU KARANTA: Mu na bayan Shugaba Buhari komai runtsi inji Jibrin

A Ranar Lahadi ne ‘Yan Sanda su ka sanar da cewa su na neman Bukola Saraki ya bayyana a gaban su bayan wasu da ake zargi da yin fashi a wani banki a Jihar Kwara sun ambaci sunan sa a matsayin mai gidan su tun lokacin yana Gwamna.

Yanzu dai Shugaban Majalisar Dattawan ya bayyana cewa ya tashi har gaban ‘Yan Sandan ya wanke kan sa. Tun da abin ya faru dai Sanatan yayi alkawarin bada hadin-kai. Bukola Saraki ya bayyana wannan ne ta shafin sa na Tuwita jiya.

A lokacin da ‘Yan Sanda su kace su na neman Sanata Bukola Saraki yayi wuf yayi magana inda yace sharri Sufetan ‘Yan Sanda yake neman sa da shi domin babu yadda za ayi a matsayin sa na Shugaba ya hada kai ayi wa al’ummar sa ta’adi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel