An damke wata mahaifiya da ta kashe jaririn ta a Sakkwato

An damke wata mahaifiya da ta kashe jaririn ta a Sakkwato

Hukumar Yan sanda na jihar Sakkwato ta damke wata matashiya Munirat Bagana mai shekaru 19 bisa zarginta da kashe jaririyarta.

Bagana, wadda yar asalin jihar Kebbi ne ta yi ikirarin cewa dama ba ta haifi jaririn da rai ba kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A yayinda ya ke gabatar da wanda ake zargin a gaban manema labarai, Kakakin hukumar Yan sandan jihar, ASP Cordelia Nwawe ta ce za'a gurfanar da Bagana a gaban kotu bayan an kammala bincike.

An damke wata mahaifiya da ta kashe jaririn ta a Sakkwato

An damke wata mahaifiya da ta kashe jaririn ta a Sakkwato

KU KARANTA: An gano kwayar da tafi haukata matasa a jihar Kano

Legit.ng ta gano cewa cikin wanda Yan sanda suka gabatar, akwai wani Nmandi Nwafor mai shekaru 32 wanda aka ce ya kware wajen satan motocci a harabar coci.

An ruwaito cewa wanda ake zargin ya kan aikata mummunar sana'arsa na satan motocci ne bayan an bi mutanen zuwa coci.

An gano cewa ya sace wata mota kirar Marsandi a wata cocin katolika da ke layin Ahmadu Bello Way a Sakkwato amma an kama shi tare da motar a Kaduna.

Kazalika, a wata rahoton, Legit.ng ta ruwaito muku labarin wata mace mai shekaru 26 da ta kashe jaririn ta mai makonni shida katchal a duniya don tana zargin shedan ne ya rikide ya zama jariri.

An dauke matar daga Senegal zuwa Newcastle tare da babban diyar ta don su hadu da mijinta. Matar tana fama da wata ciwon hauka ne mai suna Capgras Delusion wanda hakan yasa ta yanka jaririn ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel