Magoya bayan Shugaba Buhari a Majalisa sun ce babu wanda ya isa ya taba su

Magoya bayan Shugaba Buhari a Majalisa sun ce babu wanda ya isa ya taba su

- Masu kare Shugaba Buhari a Majalisa sun fara neman sa-hannun goyon-baya

- Jagoran Kungiyar Jibrin yayi karin haske yace su na tare da Shugaban kasar

- ‘Dan Majalisar na APC yace ba su da niyyar tsige Kakakin Majalisar Wakilan

A halin yanzu da ake barazanar tsige Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wasu ‘Yan Majalisar Tarayya a karkashin lemar PSG sun nuna cewa su na tare da Shugaban Kasar komin runtsin da zai shiga a Kasar.

Magoya bayan Shugaba Buhari a Majalisa sun ce babu wanda ya isa ya taba su

Kungiyar PSG a Majalisa tace tana tare da Shugaban Kasa

Honarabul Abdulmumin Jibrin wanda yake magana da yawun bakin Kungiyar PSG da ke bayan Shugaba Buhari a Majalisar Tarayya sun ce babu wanda ya isa ya ture su. Hakan ya zo ne bayan da Majalisar ta fara neman ta bincike sa.

KU KARANTA: An rufe Majalisar Tarayya sai kuma Watan gobe

Shugabannin Majalisar sun hurowa Abdulmumin Jibrin wuta bayan da yace ‘Yan Majalisar adawa ne su ke kutun-kutun na tsige Shugaban Kasa Buhari. Jibrin ya fito yayi karin bayani inda yace su ba Shugabannin Majalisan su ke hari ba.

Jibrin da ke wakiltar Kiru da Bebeji a karkashin Jam’iyyar APC yace muradun su shi ne kare Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Majalisar Taryya har ta kai sun fara neman sa-hannun sauran ‘Yan Majalisar da ke tare da Buhari.

‘Dan Majalisar da aka dakatar kwanakin baya saboda tona wasu asirin Majalisar yace sun fara neman goyon bayan ‘Yan uwan su a Majalisar ne domin marawa Shugaba Buhari baya ba wai kokarin tsige Kakakin Majalisar su ke yi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel