Yan majalisa ba za su iya razana shugaba Buhari ba - Malami

Yan majalisa ba za su iya razana shugaba Buhari ba - Malami

Alkalin alkalan Najeriya kuma ministan shari’a Justis Abubakar Malami (SAN) ya caccaki majalisar dokoki kan wasu lamuran tsigewa da suka tayar akan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya kuma ce duk sanata ko dan majalisar wakilai da aka kama da aikata laifi toh babu shakka sai hukumar da ta dace ta bincike shi.

Yace shi bai san dalilin da yasa majalisar dokoki ta nuna rashin ammana da sufeto janar na yan sanda Ibrahim Idris ba.

Malami ya bayyana zuciyarsa ne aa daren ranar Laraa yayinda yake Magana a shirin Talbijin din Channels, “The Core””, wanda Kadaria Ahmed ya gabatar.

Yan majalisa ba za su iya razana shugaba Buhari ba - Malami

Yan majalisa ba za su iya razana shugaba Buhari ba - Malami

Ministan shari’an yace maimakon majalisar dokoki ta kalualanci Buhari akan rashin tsaro da rashin aiki, kamata yayi ta gane cewa ta gaza gabatar da kasafin kudin 2018 akan lokaci.

KU KARANTA KUMA: Magoya bayan Shugaba Buhari a Majalisa sun ce babu wanda ya isa ya taba su

Idan dai bazaku manta ba a baya Legit.ng ta tattaro cewa majalisar dokoki kasar ta bukaci shugaba Buhari da ya cika wasu sharuda ta gindaya ko kuma ta tsige shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel