Madalla: Gwamnatin Buhari za ta biya Ma’aikata kudin su da ya makale

Madalla: Gwamnatin Buhari za ta biya Ma’aikata kudin su da ya makale

- Shugabar Ma’aikatar Gwamnatin Tarayya tayi wa Ma’ikata wani albishir mai dadi

- Mrs. Winifred Oyo-Ita tace Gwamnatin Buhari ta fara sakin wannan makudan kudi

- Akwai Ma’aikatan da aka karawa matsayi a wajen aiki amma ba a biya su kudin ba

Mun samu labari a makon nan cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta shirya biyan Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya wasu makudan kudin su da su ka makale cikin ‘yan kwanan nan.

Madalla: Gwamnatin Buhari za ta biya Ma’aikata kudin su da ya makale

Oyo-Ita tace Gwamnatin Buhari na daf da sakin wasu kudi

Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Winifred Oya-Ita ta a wajen wani taro na manyan Sakatarori na din-din-din na Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa Shugaba Buhari zai saki kudin da Ma’aikatan su ke bin Gwamnatin Kasar.

KU KARANTA: Kasar Amurka ta aikowa Gwamnatin Buhari wasu kudi

Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya na bin bashin wasu kudi da aka dade sun gagara fitowa. Mafi yawan kudin dai na karin matsayi ne da sauran su. Winifred Oya-Ita tace yanzu Ma’aikatan su sha kurumin su don kuwa kudi sun kusa zuwa.

Kamar yadda labari ya zo mana daga manema labarai, Winifred Oya-Ita tace Ma’aikatar kudi ta fara sakin wannan bashi na Ma’aikata. An dai shirya wannan taro ne a Birnin Tarayya domin ganin yadda za a gyara aikin Gwamnati a Kasar.

Ana ma dai neman a kara albashi a Najeriya sai dai kwanaki Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya nemi ayi la’akari da wasu muhimman abubuwa kafin a fara maganar karin albashi a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel