Babban Jigon Jam’iyyar APC a Kaduna Isa Ashiru ya sauya sheka

Babban Jigon Jam’iyyar APC a Kaduna Isa Ashiru ya sauya sheka

Mun samu labari cewa wani tsohon ‘Dan Majalisar Jihar Kaduna Rt. Hon. Isa Ashiru Muhammad ya bar Jam’iyyar APC mai mulki. Isa Ashiru yana cikin manyan Jam’iyyar a Jihar Kaduna. Kwanaki Haruna Saeed ya bar Jam’iyyar.

Rt. Isa Ashiru ya tattara kayan sa ya bar Jam’iyyar APC bayan an dade ana tunanin cewa zai fice daga Jam’iyyar. Tsohon ‘Dan Majalisar Tarayyar yace yadda abubuwa su ka sukurkuce a Jam’iyyar ta APC ta sa ya canza sheka.

Legit.ng ta ga wasikar da babban ‘Dan siyasan ya aikawa Jam’iyyar APC ta Mazabar sa da ke Kudan inda ya bayyana dalilan da su ka sa ya tsere daga Jam’iyyar. Jam’iyyar ta amince da ficewar na sa inda ta roka masa sa’a a nan gaba.

KU KARANTA: Bukola Saraki yayi kaca-kaca da Ministan Buhari a Kwara

Isa Ashiru wanda yayi takarar Gwamna a 2015 a Jam’iyyar mai mulki yace yayi tunani APC za ta kawo canjin da aka yi wa jama’a alkawari sai dai kuma aka ga Jam’iyyar wasu tsirarru kurum ta fifita don haka yace sam ba da shi ba.

Isa Ashiru ya wakilci Yankin Kudan da Makarfi a Majalisar dokoki da ta Tarayya sau 3 har zuwa 2015 inda ya nemi kujerar Gwamna. Ba mamaki dai a zabe mai zuwa Ashiru ya tsaya takarar Gwamnan Kaduna a karkashin PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel