Majalisar Dattawa sun yi kira ga Shugaban Kasa Buhari a saki sakamakon zaben 1993

Majalisar Dattawa sun yi kira ga Shugaban Kasa Buhari a saki sakamakon zaben 1993

Mun samu labari cewa Majalisar Dattawa ta dauki matakin cewa ya kamata Hukumar zabe na kasa watau INEC ta sanar da sakamakon zaben Shugaban Kasa da aka yi a Ranar 12 ga Watan Yuni a 1993.

Majalisar Dattawa sun yi kira ga Shugaban Kasa Buhari a saki sakamakon zaben 1993

Barau Jibrin ya takawa Abaribe burki na sukar Buhari a Majalisa

Hakan ya biyo baya ne bayan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya maida Ranar Damukaradiyya a matsayin 12 ga Watan Yuni a maimakon 29 ga Watan Mayu domin tunawa da zaben MKO Abiola da aka soke lokacin mulkin Ibrahim Babangida.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Majalisar Kasar ta nemi Shugaban kasa ya bayyana ainihin sakamakon zaben da har yau ba a karasa sanarwa ba sannan kuma a biya dangin MKO Abiola da Babagana Kingibe kudi da alawus.

KU KARANTA: Wani mai kudin Najeriya ya ba Buhari motocin takara

Bayan haka kuma Sanatocin sun ce Shugaban Kasa Buhari ya tabbatar da MKO Abiola da kuma Babagana Kingibe a matsayin wadanda su ka taba nasarar lashe zaben shugaban kasa da mataimakin Shugaban kasar a tarihin Najeriya.

Sai dai kuma Sanata Enyinna Abaribe ya caccaki Shugaba Buhari a kaikaice inda yace a rantsar da Ranar 31 ga Watan Disamba a matsayin Ranar da aka kashe Damukaradiyya. A wannan rana ne dai Janar Buhari ya kifar da Gwamnatin Shagari.

Dazu kun ji cewa Iyalan Marigayi Mashood Kashimawo Olawole Abiola sun ji dadin abin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi na girmama Mahaifin su da kuma tunawa da zaben da aka soke na 1993 su kace an yi masu daidai bayan shekaru.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel