An damke wata mata dake shigar ma mazauna gidan Yari tabar wiwi

An damke wata mata dake shigar ma mazauna gidan Yari tabar wiwi

Rundunar jami’an kula da gidajen yari reshen babban birnin tarayya Abuja, ta sanar da kama wata mata dake shigar ma mazauna gidan Yarin Kuje tabar wiwi, mai suna Ijeoma Joseph, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin hukumar, Humphrey Chukwuedo ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, inda yace sun kama matar ne a ranar Laraba, 6 ga watan Yuni tana dauke da tabar wiwi da ta boye shi cikin kwalin biskit.

KU KARANTA: Yaki da ta’addanci: Gwamnatin Amurka ta sanar da antaya ma Najeriya dala miliyan 102

“An kama matar ne a yayin da ta yi ikirarin kai ma wani mazaunin gidan Yarin ziyara, inda tace wani mutumi mai suna Daniel ne ya bata kwalin ta kai ma dan uwansa mai suna Miracle Amechi dake Kurkukun Kuje

“Amma da jami’anmu suka tsananta bincike sai suka gano ledojin madara, riguna, kudi naira dubu biyu da dari biyar, da kuma tabar wiwi. Sai dai Ijeoma ta yi ikirarin cewa bata san da wiwi a cikin kwalin ba.” Inji Kaakaki Humphrey.

Daga karshe Kaakakin yace tuni suka mika Uwargida Ijeoma hannun hukumar yaki da sha da ta’ammuli da miyagun kwayoyi, NDLEA, don cigaba da gudanar da bincike, sa’annan ya gargadi masu ziyara Kurkuku da su kauce ma safarar kwayoyi zuwa Kurkukun.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel